Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sake samun damar dawowa kan karagar mulkin fadar WHITE HOUSE bayan faɗuwa zaɓe a 2020. An samu bambancin hange tsakanin masu ganin zai iya dawowa da waɗanda su ke ganin ya gama mulki a ɗaya daga manyan ƙasashen duniya ko kuma a ce ɗaya daga masu ruwa da tsaki a kusan dukkan lamuran duniya kama daga tsaro, tattalin arziki, lafiya da diflomasiyya. Shin masu zaɓe sun duba muradun Trump kan kare muradun Amurka farko fiye da shiga wasu lamura na ƙasashen ketare ko dai rashin gamsuwa ga shugaba Joe Biden ne mai barin gado; za a jira a ga ko akwai wani sabon tsari na iya ruwa fidda da kai da Trump ɗin zai kawo. Hatta zuwa kotu da a ka rika yi da Trump da yanke ma sa hukuncin samun sa da laifi da hakan bai taɓa faruwa kan wani tsohon shugaban Amurka ba ya sa mamakin yadda ya kutsa har ya samu tikitin jam’iyyar sa ta Rifabulikans kuma ya yi kamfen ya sake dawowa karaga. Tun faduwar sa zaɓe ya yi alwashin zai dawo.
Wasu sun fara cewa Trump ya fahimci tunanin akasarin Amurkawa da yadda zai shawo kan su, su kauda ido kan matsalolin sa su mara ma sa baya. Ba kamar yanda Trump ɗin da ya fadi zaɓe a baya ya makale da cewa sam bai faɗi ba sai an sake ƙidaya har ma ya zuga magoya bayan sa su ka mamaye ginin majalisa CAPITOL BULIDING, ‘yar takarar jam’iyyar Dimokrats Kamala Harris ta amince da sakamakon. Ya na da muhimmanci a ga darasi na ingancin tafarkin dimokraɗiyya daga Amurka kasancewar ita mafi ƙarfin ƙasar dimokraɗiyya a duniya ta fuskoki da dama. Tuni ma Harris ta bugawa Trump waya ta taya shi murnar lashe zaɓen. A jawabin da ta gabatar a jami’ar Howard, Kamala Harris ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba kan gwagwarmayar da ta sa a gaba wato ta neman shugabancin Amurka.
A zahiri hakan ya nuna za ta sake jarraba neman takarar a zaɓe na gaba. Mataimakiyar shugabar ta Amurka ta ce za ta yi aiki wajen miƙa ragamar mulki cikin kwanciyar hankali da kenan ya saba da yanda Trump ya yi a zaben da ya kawo ta fadar da shugaba Biden. Ba mamaki tusfar shugaba Biden ko rashin kazar-kazar ya jawo harris ta samu tangarɗa. Hakanan rashin sanin za ta zama ‘yar takara a kan lokaci ya sa ba ta shirya sosai wajen yin kamfen ba. Yayin da nasarar Trump za ta zama abun mamaki in an duba siradin da ya tsallake, a gefe guda faɗuwar Harris ba ta zama abun mamaki ba. Ba zan karfafa masu tunanin kasancewar Harris mace ba ne ya jawo faɗuwar don Amurka ba lallai ta na nuna bambancin maza da mata ba ne.
A tarihi dai mace ba ta taɓa jagorantar Amurka ba amma ba ya na nuna hakan don kasancewar ’yan ƙasar ma sun ɗau mata cewa ba su cancanci shugabancin dimokraɗiyya ba ne. In mun duba ma mata kan zama kan gaba a mulkin mazajen su misali Hillary Clinton, Michelle Obama da sauran su. Ita Michelle ma an dauka za ta samu takarar da Harris ta yi sai daga bisani abun ya canja. Kuma Michelle ce kan zama mai gabatar da mijin ta tsohon shugaban Amurka Barack Obama a wasu taruka ko ma a jawabin da ya gabatar na mara baya ga takarar Kamala Harris.
Wani dai muhimmin abu a nan duk da Trump na fitowa da matar sa amma ba ta taka gagarumar rawa kan siyasar sa kuma hakan na da nasaba da yanayin Trump ɗin kan mata ko rashin salo na matar ta sa Melania. A wani jawabin ta ma a can baya, Melania ta so kunyata mijin na ta. A jawabin Trump na wannan karon na murnar samun nasara ya godewa Melania da aiki tuƙuru da ta yi na kamfen. Wani abu mai ban sha’awa game da dimokraɗiyyar Amurka shi ne samun sauyin gwamnati tsakanin Demokrats da Rifabulikans.
’Yan Nijeriya na cigaba da tattaunawa kan babban zaɓen Amurka da a ka gudanar da zaɓen a Talatar nan.
Masu sharhin sun fi karkata ne kan fatan sakamakon zaɓen ya zama ya kare muradun ƙasashe masu tasowa.
Tasirin Amurka a tattalin arziki, tsaro da siyasar duniya ya sa tamkar babban zaɓen ƙasar ya shafi hatta waɗanda ba su da hurumin kaɗa ƙuri’a.
Ga ɗaya daga shugabannin jiha na ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ Farouk Mu’azu har yanzu Amurka na jan zaren ta a kowane fanni na lamuran duniya.
Hakanan shi ma tsohon shugaban ƙungiyar matasa ta Nijeriya NYCN Murtala Garba na cewa ya na da muhimmanci kyautata fatar daidaituwar dimokraɗiyya a Amurka don zama darasi ga sauran ƙasashen dimokraɗiyya “dole ne mu yi wa Amurka fatan alheri duk abun da zai shigo Amurka ya zama mai dama-dama don mu samu zaman lafiya. Don ko mutum ya ƙi, a yanzu kam helkwatan duniya na Amurka ne”
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Farouk BB.Farouk ya duba sharhin da jama’a ke yi inda ya aza bisa mizani da yadda a ke samun akasi a Afurka “sai mu ke ganin ga wasu al’adu nan da an fi ganin su a ƙasashe masu tasowa ko ƙasashen da a ke yi mu su kama karya na shugabanni wanda su ke zama har abada sun fara nunawa a dimokraɗiyyar Amurka”
Wani muhimmin lamari a sharhin shi ne zaman dindindin na ‘yan siyasar Amurka a jam’iyyun su duk da hakan ba ya hana wasu daga cikin su cin gajiyar ‘yancin marawa dan hamaiyar su baya, wanda hakan kamar a nan Nijeriya sauya jam’iyya tamkar sauya riga ne.
Gabanin gudanar da zaben na shugaban Amurka, hankalin masu sharhi da dama daga ‘yan Nijeriya ya koma kan shirin zacɓen.
Hakan ba zai rasa nasaba da tasirin Amurka kan ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya ba irin Nijeriya da ke bin tsari daya da na Amurka.
Kama daga cikin motocin fasinja, shagunan kasuwanni zuwa majalisun zaman jama’a da shirye-shiryen siyasa na kafafen labaru, batun zaɓen na Amurka na daga muhimman lamuran da a ke tattaunawa.
Tsohon jakadan Nijeriya a Trinidad da Tobago Hassan Jika Ardo ya duba yadda jama’a ke zayyana ‘yan takarar biyu Kamala Harris ta Dimokrats da Donald Trump na Rifabulikans “Kamala Harris ta na nuna cewa duk wani Ba’Amerke ya na da ‘yanci kuma za ta lura da shi ko da bai zaɓe ta ba. Shi kuma Donald Trump harkar tattalin arziki ya na riƙe da shi.
Shi kuma masanin harkokin siyasa n jami’ar Abuja Dr.Farouk BB.Farouk ya duba muradaun tattalin arziki ne da salon rayuwa kan zaɓen na Amurka ga ƙasashen Afurka “mu na kallon zaɓen Amurka zai zo ma na da ɗaya daga waɗannan makomar ko ya kawo ma na ‘yan Rifabulikan da za su zo su damu da abubuwan tattalin arziki duk da Trump ba wai ya damu da Afurka ba ne, ko dai ‘yan Dimokrats za su zo kasancewar Kamala Harris macece ta yarda da al’adu na dabbaka fifikon mata da kuma yarda da auren jinsi da sauran su. Ba mu da tabbas kan wane ne zai iya zama”
Duk da waɗannan bayanai masanin harkokin siyasa na jami’ar Bayero ta Kano Dr.Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kusan duk ‘yan takarar a manyan muradu na da aƙida iri daya in ban da bambanacin yanayin aiwatarwa “kowane gauta ja ne indai a siyasar Amurka ne. Wataƙila in wane ne ya ci zai dafa ‘yan Afurka da ruwan zafi, in wane ne ya ci zai dafa Afurka da ruwan sanyi.
Amanna da cewa murdiyar aringizon ƙuri’u ba ta tsarin zaɓen Amurka kamar yanda a ke zargi a Nijeriya; abun fata jagoran dimokradɗiyya ya zama zaɓin jama’a.
Kammalawa;
Babban abun da yanzu za a fuskanta ko fata shi ne matakin da a ke sa ran Donald Trumo zai dauka na daidaita lamura a Gaza. Zubar da jinin da a ke yi a Gaza ya zama babban abun takaici da rashin gamsashshiyar amsa a duniya. Trump na dawowa karaga daidai lokacin da Firaministan Isra’ila ke ƙara daura damarar yaƙi a irin tunanin sa In an duba yanda ya sauke ministan sa na tsaro Yoaɓ Gallant a wani mataki da ya ba da mamaki.
Dama ba tun yanzu ba Netanyahu ke son sallamar Gallant amma ya dakata don har zanga-zanga jama’a su ka yi kan a bar Gallant a kan kujera.
Netanyahu ya ce ya yi ƙoƙarin daidaita bambance-bambancen sa da Gallant amma abun ya ƙi yiwuwa.
A ra’ayin Netanyahu ya na da kyau a yanayin yaƙi Firaminista da ministan tsaro ya zama su na tafiya a matsaya ɗaya.
Za a maye gurbin Gallant da ministan waje Israel Katz wanda mai biyaiya ne ga ra’ayoyin Netanyahu. A nan ya nuna Netanyahu na son ‘yan amshin shatan sa kaɗai za su kasance a gwamnatin in ya ce baki su ce kirim. Shin Trump zai iya dakatar da wannan kisan kare dangin kamar yanda ya yi alwashi a kamfen ko kuwa a’a za a jira a ga sabon kamun ludayin sa. Ko yau a ke dakatar da yakin Gaza an riga an tabka barna da asarar fiye da mutum 40,000.
