Okpebholo ya naɗa ɗan Oshiomole a matsayin Kwamishinan Lafiya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebolo, ya naɗa Dr Cyril Adams Oshiomhole a matsayin kwamishinan lafiya.

Cyril ɗan Adams Oshiomhole ne, tsohon gwamnan Edo, wanda yanzu ya zama sanata mai ci. An kuma naɗa Barista Musa Ikhilor a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG) da Honorabul Samson Osagie a matsayin babban lauya kuma kwamishinan shari’a.

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Edo, Fred Itua ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Majalisar dokokin jihar Edo za ta tabbatar da naɗin Osagie da Oshiomhole lokacin da Gwamna Okpebolo ya gabatar da su nan ba da daɗewa ba.”

Dokta Cyril Adams Oshiomhole ya fara karatunsa ne a makarantar firamare ta St. Anne, sai kuma Command Secondary School, inda. Daga nan ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digirinsa na farko a fannin likitanci da tiyata (MBBS).

Oshiomhole ya yi rajista a Makarantar Kiwon Lafiyar Jama’a da Magunguna ta Jami’ar Tulane, New Orleans, LA. inda ya samu digiri na biyu na Kimiyya a Kiwon Lafiyar Jama’a (MSPH, wanda ya fi girma a Kiwon Lafiyar Muhalli, Toɗicology, and Disaster Management).

Neman karatunsa ya ci gaba a Jami’ar Harɓard, Boston, inda ya samu horo na digiri na biyu a Clinical Research da kuma Jami’ar ƙueen Mary, London, inda ya karanta Gastroenterology.

By ukarofi