Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Rukuni na 4 daga cikin Rukunai 50 na marayun nan su 174 da aka ɗauko lokacin tsananin rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe, waɗanda fitaccen ɗan kasuwar nan mai taimakawa marayu wanda ake yi wa laƙabi da Uban Marayu Dr. Ummarun Kwabo yake ɗaukar nauyin kula da su ƙarƙashin kulawar Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, sun samu nasarar komawa gida, bayan da suka kammala aikin Umra da aka kai su.
Shugabar makarantar da ke kula da ilimantar da waɗannan yara marayu maza da mata Malama Adama Muhammad ta bayyana cewa, shekaru kimanin bakwai kenan ana kula da waɗannan marayu. Ta ƙara da cewa, kawo yanzu wannan shi ne rukuni na huɗu daga cikin marayun da suka samu haddar Alƙur’ani Mai Girma, waɗanda Uban Marayu Alhaji Ummarun Kwabo, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin kai su Umra.
Dukkan ɗaliban da suka je ƙasa mai tsarki, sun kammala ziyararsu lafiya sun kuma dawo gida lafiya, in banda wasu ɗalibai 3 daga cikinsu da suka je ganin likita. Sannan kuma akwai shugabannin makarantar da wasu masu hidimar marayu mutum goma da su ma aka ta fi da su Umrar, domin kula da ɗaliban.
Shugaban Kwamitin Amintattun Makarantar, Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, da Alhaji Sanusi Ummarun Kwabo Ciroman Jarma, suna daga cikin waɗanda ke tare da ɗaliban yayin tafiyarsu tun daga Sakkwato har zuwa ƙasa Mai Tsarki.
Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Aliyu da malaminsu Alkur’ani, Malam Zaharadden, sun bayyana godiya akan kulawar da ake bai wa waɗannan marayu.
