Wani abin mamaki ya faru yayin da mahaifi mai shekara 52 ya kashe ‘ya’yansa uku, ya ɓoye gawarwakinsu a cikin firiji.
Rundunar ’yan sanda a Enugu ta kama wani Ifeanyi Amadikwa, mai shekaru 52, da laifin kashe ‘ya’yansa tare da jefar da gawarwakinsu a cikin wani lalataccen firiza.
Jaridar The Cable ta ruwaito rundunar ‘yan sandan ta ce, wanda ake zargin ya haifi biyu daga cikin yaran yayin da yaro na uku kuma ’yar matarsa ce.
Bayanai sun nuna cewa, an bar yaran a hannun wanda ake zargin ne a ranar Talata, 4 ga watan Janairu daga hannun mahaifiyarsu, wadda ta tafi kasuwa.
Daniel Ndukwe, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Enugu, a wata sanarwa a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, ya ce, an gano yaran a cikin firij da raunuka a yayin bincike.
A cewar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya jawo kawar da hankalin mahaifiyar kan duba firij ɗin a lokacin da ta ke neman yaran.
Ndukwe ya bayyana a ƙarshe cewa, “an ga gawarwakin yaran a cikin firij da raunuka, wanda ke nuni da cewa an kashe su ne aka jefa su cikin firiji.”
Nan take aka kai gawarwakin zuwa asibiti inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsu, sannan aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawa domin adanawa da kuma tantance gawarwakin.
