ECOWAS ta bai wa Burkina Faso, Mali, da Nijar wa’adin watanni shida don sake duba matsayarsu kan ficewa daga kungiyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Lamarin ya biyo bayan taron da shugabannin Ƙungiyar raya Tattalin Arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) karo na 66.

Sabon wa’adin zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa 29 ga Yulin 2025.

Hakan na nufin ƙofofin ECOWAS za su kasance a buɗe ga ƙasashen uku har zuwa lokacin da za su fayyace matsayarsu kan ko za su dawo ko kuma sun tafi kenan.

Idan ƙasashen suka tabbatar da ficewarsu, hakan na iya tasiri ga yankin ta fannin tattalin arziki, da diflomasiyya, da tsaro, kuma ka iya kawo cikas ga zirga-zirgar mutane da kayayyaki musamman na kasuwanci wanda zai ta’azzara rashin daidaito kan harkokin tattalin arziƙi.

Ƙasashen uku sun kulla sabuwar kawance tsakaninsu mai taken; ƙawancen ƙasashen Sahel (AES), da nufin samar da haɗin-gwiwa a fannin tsaron iyakoki.

Shugabannin na ECOWAS sun kuma yaba da ƙoƙarin da Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal da takwaransa na ƙasar Togo, Faure Gnassingbé kan rawar da suka taka wajen ganin sun dawo da ƙasashen uku cikin kungiyar.

Ƙungiyar ta kuma ƙara wa’adin jagorancin shugaban ƙasar Togo da na Senegal na cigaba da aikin shiga tsakani har zuwa ƙarshen wa’adin da ta bai wa ƙasashen.

By Babaji