Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta yanke shawarar gayyatar babban hafsan tsaron Ƙasar, Shugaban Sojojin Ƙasa da kuma kwamandan bataliya ta 177, saboda zargin kamawa da tsare wani shugaban al’umma ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Nasarawa.
Ɗan majalisa Mansur Soro ne ya gabatar da ƙudirin a zaman majalisa na ranar Talata, inda ya bayyana cewa a ranar 9 ga Disamba, 2024, sojojin bataliya ta 177 sun kama Bello Badejo a garin Maliya na jihar Nasarawa ba tare da an yi masa wata takardar gayyata ko umarnin kotu ba.
Ya ƙara da cewa, har zuwa mako guda bayan kamun, har yanzu ba a gurfanar da Badejo a gaban kotu ba, wanda hakan ya saɓawa doka, kuma take haƙƙin bil’adama ne kamar yadda sashe na 34, 35 da 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanada.
Shugabannin tsaron za su bayyana a gaban kwamitocin Majalisa na Sojoji, Hakkokin Ɗan Adam, da Shari’a a ranar Alhamis, 20 ga Disamba, 2024 domin yin bayani kan lamarin.
