Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan aikin Gona ta kasa reshen jihar Kano, wato ‘Nigerian Union of Agriculture and Allied Employees’, (UNAAE) ta ƙaddamar da shugabannin shiyyoyin ƙungiya da za su jagoranci yankinsu na wata uku,
A jawabinsa, Manajan darakta na hukumar aikin Gona na jihar Kano KNARDA Dr. Faruku Kurawa wanda daraktan Istanshan na KNARDA Gambo Isa Garko ya wakilta, ya yaba da shugabannin riƙo na ƙungiyar reshen jihar Kano da suka zaɓo waɗannan jajirtattun kiyateka,
Ya kuma ja hankalin waɗanda aka naɗa da su fahimci cewa riƙon kwarya aka ba su ba na dindindin ba ne, su yi ƙoƙari idan akwai wasu kura-kurai da aka yi a baya to su gyara su ta yadda zai zama idan zaɓaɓɓun shugabannin suka zo za su samu sauƙin tafiyar da ƙungiyar.
Tunda farko a jawabinsa, Comrade Zaharadden Abdullahi Yakasai ya bayyana rantsar da kiyatekar a matsayin babbar nasara.
Ya ƙara da cewa, “Mun rantsar da shugabannin rassan da muke so su yi shi ne su bi hanya sahihiya don gudanar da zabe a nan gaba, don ciyar da su gaba da kuma kyautata harkar aiki.”
“Mun ba su dama ga duk wanda ya ke da sha’awar ya shubabanci maaikatarsa ya fito ya tsaya mutane su zaɓe shi.
“A cikin membobin ƙungiya fiye da mutum dubu aka zaɓo su aka ba su wannan mukami, don haka nake kira a garesu da su yi adalci kuma su riƙe amana su ji tsoron Allah,” inji kwamared Abdul’azizBlueprint Manhaja ta ruwaito cewa, shugabannin da aka rantsar za su yi wata uku suna jan ragamar ƙungiyar Manoma ta UNAAE, sannan
tana da membobin sama da 3,000 a cikin rassan na Jihar Kano bakiɗaya
