Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da ’Yan Sanda ta ƙasa (PSC) ta amince da naɗin sabbin kwamishinonin ’yan sanda guda shida.
Game da naɗin da canja wuraren aiki, PSC ta ce ya biyo bayan ƙarin girma da hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta yi wa wasu jami’ai a makon jiya.
A cikin sabbin naɗe-naɗen, an tura CP Shettima Jauro Mohammed zuwa rundunar jihar Nasarawa; Rabin Mohamned, yanzu CP, kwamandan jihar Kaduna da Adepoju Olugbenga Adewale aka tura zuwa rundunar jihar Ribas.
Sauran su ne; Mohammed Baba Azare, yanzu CP, Kwamandan Jihar Akwa Ibom; Wilfred Olatokunbo Afolabi sabon CP Ondo State Command da Joseph Eribo, tsohon CP, jihar Akwa Ibom yanzu sun koma jihar Ekiti a matsayin sabon kwamishina na jihar Ekiti.
A cewar wata sanarwa da shugaban hukumar, DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), ya fitar ranar Talata ta hannun shugaban yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Ikechukwu Ani, ya ce sabbin waɗanda aka naɗa ya kamata su ga naɗin nasu a matsayin kira ga yi wa ƙasa hidima.
Argungu ya roke su da su jajirce wajen ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma tare da tabbatar da cewa jihohin mu sun samu raguwar aikata laifuka.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan rahoton ci gaban da suka samu tare da ƙarfafa musu gwiwa don samun nasara a sabbin ayyukan da suke yi.
Shugaban PSC ya buƙace su da su mayar da martani ga gwamnati ta hanyar sadaukar da kansu ga hidimar ƙasarsu.
