Hukumomin ƙasar Zambiya sun kama wasu mutune biyu, waɗanda ake zargin su ”matsafa” ne da aka bai wa aikin asirce shugaban ƙasar, Mista Hakainde Hichilema.
’Yan sanda sun ce sun kama Jasten Mabulesse Candunde da Leonard Phiri a Lusaka, babban birnin ƙasar.
“Aikin da suka ƙudiri aniyar yi shine amfani da layu wajen cutar da shugaba Hakainde Hichilema,” kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta bayyana.
Mutane da dama a ƙasar da ke kudancin Afirka sun yi amanna da bokaye, inda a lokuta da dama mutane kan rayu da fargabar tsoron asiri.
‘Yan sanda sun yi zargin cewa Nelson Banda – ƙanin wani ɗan majalisa Emmanuel Banda, da aka fi sani da “Jay Jay” Banda – ne ya bai wa bokayen aikin sabauta shugaban ƙasar.
A watan da ya gabata ne aka kama ɗan majalisar a makwabciyar ƙasar Zimbabwe kan zargin laifin fashi, zargin da ya musanta.
Sanarwar ‘yan sanda ta ce wanda ake zargi da bai wa bokayen aikin ya tsere, inda suka alƙawarta farauto shi.
An dai kama bokayen ƙarƙashin dokokin tsafi na ƙasar, inda ake zarginsu da aikata tsafi da zaluntar dabbobin, bayan da ka same su da tarin guraye da layu da kuma hawainiya da ranta, kamar yadda ‘yan sanda suka yi bayani.
Bokayen sun kuma bayyana wa ‘yan sanda cewa an yi musu alƙawarin kuɗin ƙasar fiye da kwaca miliyan biyu kimanin dala 73,000, idan suka kammala aikin sabauta shugaban ƙasar.
