A ranar Litinin da ta gabata ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin wasu ’yan jarida a gidansa da ke Legas domin tattaunawa da su wanda ya ɗauki kusan awa ɗaya ana yi.
Wannan shi ne karon farko na irin wannan mu’amala da ’yan jarida da ya taɓa yi tun bayan da ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Tattaunawar shugaban ƙasa da ’yan jarida ya kasance abin da aka saba yi a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo. Tattaunawar ta ba shi damar yin magana kan wasu muhimman batutuwan ƙasa. Har ila yau, ta ba shi dama wajen warware wasu batutuwan da ke tada hankulan ‘yan Nijeriya da dama dangane da manufofinsa da shirye-shiryensa da salon mulkinsa.
Matakin da shugaba Tinubu ya ɗauka na karɓar baƙuncin tattaunawar ya bai wa ‘yan Nijeriya da dama mamaki. Ya kasance al’adar shugaban ƙasa ya yi magana da al’ummar ƙasar ne kawai a wasu lokuta na musamman kamar ranar tunawa da ‘yancin kai da kuma ranar sabuwar shekara. Kamar yadda ake tsammani, ‘yan Nijeriya sun yi ta mayar da martani game da batutuwan da shugaban ya yi magana dangane da shirye-shirye da manufofin da gwamnatinsa ta ɓullo da su. Daga ciki har da cire tallafin man fetur da kuma batun Naira a kasuwannin hada-hadar kuɗi da ake kyautata zaton cewa ya kawo cikas ga tattalin arzikin da tuni ya durƙushe, wanda hakan ya janyo wa ‘yan ƙasa kƙncin da ba a taɓa ganin irinsa ba.
Martani game da tattaunawar sun bambanta. Yayin da wasu ke bayyana amincewa da matakan a matsayin hanyƙ ɗaya tilo ta fitar da tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa, wasu kuma na ganin cewa matakan shugaban kamar “yi wa majiyyaci tiyata ne ba tare da allurar kashe zafi ba”.
Sanin al’umma ne cewa babu wani shugaba kafin Tinubu da zai iya ɗaukar irin wannan mataki. Gwamnatocin baya sun yi ta doje wa batun cire tallafin man fetur wanda daga ƙarshe ga ta ta zo. An yi imanin cewa da a ce an ɗauki matakin tun da farko, da al’ummar ƙasar ba au shiga ƙangin da suka samu kansu a halin yanzu ba. Ba tare da shakka ba, daga cikin illolin cire tallafin akwai hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka. Sai dai shugaban ya tsaya a kan bakarsa, yana mai jaddada cewa gyare-gyaren ya zama dole domin samun ci gaba na dogon lokaci.
Ya ce, “A shekaru mun ƙarar da albarkatunmu wajen bayar da tallafi da shirye-shirye marasa ɗorewa. Cire tallafin man fetur ya kasance al’amari ne mai muhimmanci. Ba abu ne mai sauƙi ba, amma ya zama dole don hana tattalin arzikin ƙasar durƙushewa. Dole ne mu sarrafa albarkatun mu ta hanyoyi daban-daban kuma mu mai da hankali kan zuba jarinnda zai tabbatar da wadatar ƙasa. Tabbas, akwai zafi, kamar naƙuda ne, matakin da ke kaiwa ga haihuwar ɗa mao kyau. Ina da yaƙinin cewa manufofinmu na yanzu suna aza harsashin samun kyakkyawar makoma.
Wani batu da ya ƙara jan hankali a yayin tattaunawar shi ne matsayin shugaban ƙasa a kan ƙudurorin sake fasalin haraji da ake cece-kuce a majalisar dokokin ƙasar a halin yanzu. ƙudurorin, wato ‘Najeriya Taɗ Bill 2024, Nigeria Taɗ Administration Bill 2024, Joint Reɓenue Board of Nigeria’ (Establishment) 2024, ‘Nigeria Reɓenue Serɓice’ (Establishment) 2024, na da nufin gyara yadda ake tafiyar da harkokin haraji da rabon kuɗaɗen ƙasar.
Ya yi nuni da cewa, wannan sauye-sauyen na goyon bayan talakawa ne, kuma an tsara shi ne domin faɗaɗa hanyoyin biyan haraji, yana mai jaddada cewa, alamar shugaba nagari shi ne iya yin abin da ya kamata a lokacin da ya kamata. Ya bayyana shirye-shiryen gwamnatinsa na yin sassauci kan kuɗaɗen haraji tare da jaddada buƙatar kawar da harajin da aka yi tun zamanin mulkin mallaka ta hanyar maye gurbinsu da tsarin haraji na zamani wanda ya dace da yanayin tattalin arziki da ake ciki a yanzu.
Haka kuma a wurin tattaunawar akwai batutuwan da suka shafi rashin tsaro da cin hanci da rashawa wanda shugaban ƙasar ya amince cewa su ne manyan ƙalubale da al’ummar ƙasar ke fusktanta. Yayin da yake lura da girman matsalolin cin hanci da rashawa, ya bayar da hujjar cewa magance su “yana buƙatar tsarin da ya dace.”
Rashin tsaro ya ci gaba da zama ruwan dare a faɗin ƙasar duk da kasafin kuɗin da ake keɓewa a duk shekara don yaƙar wannan barazana saboda al’ummar ƙasar na fuskantar ƙalubalen ƙarni na 21 da hanyoyin da suka shuɗe. Yayin da ake maraba da kafa rundunar ‘yan sandan jihar da za ta tabbatar da samun ƙarin tsaro da zai mamaye ko ina, dole ne gwamnati a dukkan matakai su rungumi amfani da fasahohi kamar jirage marasa matuƙa don ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin jami’an tsaro. Haka kuma an imanin cewa har yanzu satar mutane don neman kudin fansa na ci gaba da haɓaka duk da cewa masu aikata laifin suna tattaunawa da wayoyin hannu da ya kamata hukumomin tsaro su bi diddigin su.
A taƙaice dai, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi a ƙoƙarinta na magance wahalhalun da ke addabar talakawa. Shirye-shiryen motoci masu amfani da gas da abubuwan hawa masu amfani da wutar lantarki babban ci gaba ne ga gwamnatin Tinubu a cikin sauran matakan da suka shafi mutane da aka gabatar zuwa yanzu. Ya kamata a ƙara musu ƙarfi. Har ila yau, abin farin ciki ne ganin yadda farashin man fetur ke sauka a hankali a sakamakon tace man a cikin gida. Hakan zai ƙara haɓaka darajar Naira a kasuwannin hada-hadar kuɗi.
