Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ayyana ɓarkewar annobar Korona a ƙasar Sin a matsayin lamari mai buƙatar gaggawa.
Babban daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Geneva.
Kwamitin WHO kan wannan annoba ya gudanar da taro a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka bada shawarar ayyana wannan ɓarkewar a matsayin babbar matsalar lafiya da ke buƙatar gaggawa (PHEIC).
Shugaban kwamitin, Didier Houssin, ya bayyana cewa shawarar da aka yanke kusan duka membobi ne suka amince da ita a taron.
A cewar Tedros, “Babban dalilin wannan ayyanawa, ba abin da ke faruwa a ƙasar Sin ba ne, sai dai abin da ke faruwa a sauran ƙasashe.” Ya ƙara da cewa, “Babban damuwar mu shi ne yiwuwar cutar ta yaɗu zuwa ƙasashen da ke da rauni a fannin kiwon lafiya kuma ba su shirya tsaf don tunkarar wannan ƙalubale ba.
Wannan sanarwa ba tamkar rashin amincewa da ƙoƙarin ƙasar Sin ba ne; a’a, muna da cikakken yaƙinin kasar Sin za ta shawo kan wannan annoba.”
Tedros ya bayyana wasu daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar don daƙile annobar, ciki har da gaggauta samar da rigakafi da magunguna da kuma yaƙar yaɗa bayanan ƙarya game da cutar.
