Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa ɗansa, Abdulwahab, da mahaifiyarsa, Hajiya Maryam, sun rasu kimanin mako guda da auren ɗiyarsa, Fatiha.
Idan za a iya tunawa, ɗan gwamnan ya rasu a makon da ya gabata a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi sa’o’i 24 kacal bayan mahaifiyarsa ta rasu sakamakon rashin lafiya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Yahaya, ya jagoranci tawagar da suka kai ziyarar jaje a garin Kafin Hausa da ke Jihar Jigawa, domin jajanta wa Namadi.
A nasa jawabin, gwamnan na Jigawa ya gode wa takwaransa na Gombe da suka tsaya masa a lokutan jimami, inda ya ce Yahaya ma ya halarci ɗaurin auren ’yarsa, mako guda kafin afkuwar lamarin.
“Gwamna, mako guda da ya gabata, kana jihar Jigawa domin halartar bikin ɗiyata Fatiha, kuma yanzu ka zo nan don jajanta mana kan rasuwar mahaifita da ɗana. Wannan yana nuna ƙaunar ku gare mu da salon jagoranci na musamman. Ba za mu iya gode maka ba, Gwamna,” inji Namadi.
“Allah Ya karɓi abinSa ne, domin kowane abu yana faruwa ne bisa nufinSa. A matsayinmu na Musuli, mun yi imani da gaske cewa ba za a iya wuce ƙaddarar Allah ba. A kan wannan batu, ina roƙon ku da ku dage kuma ku rungumi ƙaddarar Allah.
“A madadin ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa da gwamnatin jihar Gombe, ina mika saƙon ta’aziyyarmu ga ku da al’ummar jihar Jigawa. Allah ya gafarta musu, ya saka musu da Aljannar Firdausi,” inji Yahaya.
