Jami’an tsaro sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Baƙo Baƙo da wasu yaransa a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jami’an tsaro sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Baƙo Baƙo da wasu yaransa dake cikin dabar ɗan bindigar.

Baƙo Baƙo na cikin jerin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro ke nema ruwa a jalo, lamarin ya faru ne bayan wani samame da jami’an tsaron haɗin gwiwa suka kai a dazuzzukan ƙaramar hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

A cewar majiyoyin tsaro, wani samame na haɗin gwiwa da ya haɗa da sojoji, da ‘yan sandan, da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence da kuma jami’an tsaron al’umma ne suka kutsa cikin maɓoyar ‘yan bindigar da yammacin ranar Larabar da ta gabata, inda suka yi artabu da ɓarayin, lamarin dai ya yi sanadiyyar kashe Baƙo Baƙo wanda ya addabi al’umar Jihar Katsina musamman a yankin ƙaramar hukumar Batsari.

Baƙo ya shahara wajen kitsa munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da ta’addanci a faɗin jihar, musamman ga mazauna ƙaramar hukumar Batsari.

Tuni mazauna yankin suka fara nuna jin daɗin su game da tarwatsa dabar Baƙo da yaransa waɗanda ke sace mutane don neman kuɗin fansa.

“Wannan babbar nasara ce ga al’ummarmu. Muna matuƙar godiya da ƙoƙari da sadaukarwar da sojojin suka yi don dawo da zaman lafiya a yankinmu,” in ji wani shugaban al’umma a yankin Batsari.

Jami’an tsaron dai sun kutsa kai dabar ‘yan bindigar yayin da dare ya soma yi. Bayan musayar wuta mai tsananin gaske tsakanin ɓangarorin biyu jami’an tsaron sun yi nasara sakamakon nuna ƙwarewar aiki da suka yi inji majiyarmu.

By ukarofi