Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tun fara yakin Gaza a ranar 7 ga Oktobar bariya wato 2023 hakan ya zama shi ne mafi girman labarin zubar da jini da ke mamaye kafafen labarun duniya duk da hakan bai kawo dakatar da yaƙin ba. Da zarar ka ji sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya garzaya gabar ta tsakiya to batun na Gaza ne. Mun sha nanata yawan mutanen da su ka mutu a Gaza da su ka haura mutum dubu 40 kuma akasarin su mata ne da ƙananan yara. Abun damuwa a yaƙin shi ne yadda fararen hula su kan kwana su tashi da ido biyu buɗe don kowane lokaci za a iya kawo hari ta jiragen sama da za a samu asarar rayuka. Shin ma akwai wani iyali a Gaza da bai rasa wasu ‘yan uwa ba? Zai yi wuya kuma a kan ma iya samun iyalin da ba mamaki an ma kashe su gaba ɗaya. Wasu gawawwakin ma ba a iya samun su ba balle a je ga batun yi mu su jana’iza don an haƙiƙance akwai mutanen da gine-gine su ka rufta kan su kuma ba a samu damar tono su ba. Burin Isra’ila na murƙushe Hamas na nuna neman ƙarar da dukkan al’ummar Gaza da ma Falasɗinawa. Ai ‘yan Hamas ba wasu mutane ne daban ba ko waɗanda su ka faɗo daga sama a’a ‘yan Gaza ne mutane kuma Falasɗinawa.
Kazalika mun san cewa Isra’ila ta kashe shugaban Hamas Isma’ila Haniyeh a Tehran inda ta sake kashe wanda ya maye gurbin sa Yahaya Sinwar a Gaza. Dama duk wanda ya amshi ragamar jaograntar Hamas ya dace ya ajiye likkafanin sa ko ma ya riƙa yawo kusa da makara! Haka Isra’ila ta kashe jagoran Hamas Ahmad Yassin lokacin da ya ke tafiya sallar asuba kan keken guragu. Isra’ila ba ta bar ɗaya jagoran ba Abdul’aziz Rantisi. Don haka in don kashe shugabannin Hamas ne zai zama murƙushe Hamas to da tuni ƙungiyar ta mutu murus. Isra’ila ta kama dubban matasan Falasɗinawa ta zuba a gidajen yarin ta. Tun kafa ƙasar Isra’ila daga yankunan Falasɗinawa a 1948 ba a sake samun sararawar Falasɗinawa ba. Ko shugabannin ƙasar Falasɗinu da ke Ramallah ba wani zaman lafiya su ka samu ba duk da gwagwarmayar su ta baki ne. Wannan ya nuna kowane zaɓi Bafalasɗine ya ɗauka ba shi da tabbacin samun zaman lafiya. Rahotanni na nuna shi kan sa shugaban Falasɗinawa Yassar Arafat ba mutuwar salun alun ya yi ba an ƙulla maƙarƙashiya. A nan sai dai Falasɗinawa su amince da zama bayin Isra’ila su kuma sadaukar da ƙasar su ga Isra’ila sannan ne za su iya zama ba tashin boma-bomai. Ina amfanin baɗi ba rai. Wato gaskiyar magana duk wanda zai nunawa Isra’ila yatsa cewa ta mamaye yankin Falasɗinawa sai Isra’ila ta ɗau matakin karya yatsar kuma ba wani matakin da duniya za ta ɗauka ya yi wani tasiri. Ba ma mun kawo mu ku cewa har kotun duniya ta yanke hukuncin dakatar da Isra’ila daga kisan kiyashi a Gaza ba da ma ayyana neman Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu don fuskantar laifukan yaƙi? Haƙiƙa Isra’ila ta shashantar da wannan mataki na kotun duniya da nuna sam ba wani tasirin da hakan zai yi. Isra’ila ce kusan kasa ɗaya tak da kan kai hari kan wata kasa ba tare da jin shakkar wani abu zai biyo baya ba. Mu duba cigaba da hare-hare cikin Siriya duk da kawar da gwamnatin Bashar Al’asad da sunan wargaza makaman jama’ar tsohon shugaban. ƙasar dai na da goyon bayan masu faɗa a ji a duniya don haka ta ke cin Karen ta ba babbaka. Abu dai ɗaya tak shi zalunci ba zai zauna har abada bai kau ba.
ƙungiyar Hamas mai gwagwarmayar kwato ’yancin Falasɗinawa ta na buƙatar samun tsagaita wuta kan yaƙin Gaza ba da ɓata lokaci ba.
Babban jami’in Hamas Basem Na’im ya bayyana hakan da ba da tabbacin an dawo da tattaunawa a birnin Doha don cimma yarjejeniyar.
ƙatar, Masar da hadin kan Amurka ke jagorantar sa baki don cimma matakin tsagaita wuta a yaƙin da ya haura shekara ɗaya a na asarar ran akasarin mata da ƙananan yara.
Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce an ba da umurnin wakilan Isra’ila su shiga yarjejeniyar.
Isra’ila dai na jan kafa ne kan yarjejeniyar da za ta kai ga dakatar da yakin gaba daya da buƙatar ‘yan dabaru da hakan zai ba ta damar cigaba da kai hare-hare da sunan murƙushe Hamas.
A na zargin juna da kafa sharuɗa masu tsauri da ke kawo cikas ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila.
Yayin da Hamas ke son Isra’ila ta dakatar da dukkan hare-hare da janyewa kakaf daga Gaza gabanin sako kamammu, Isra’ila na cewa sai ta karbo duk mutanen ta da ke hannun Hamas da wargaza Hamas ɗin kafin dakatar da yaƙi.
Wannan na zuwa ne gabanin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump a ranar 20 ga watan nan inda ita ma gwamnatin Joe Biden mai barin gado ke neman cewa ta na yunƙurin samar da maslaha a ‘yan kwanakin ta ƙalilan da su ka rage a fadar White House.
Donald Trump ya gargaɗi Hamas da ta sako dukkan kamammun Isra’ila da ke hannun ta kafin a rantsar da shi, ya na mai kurarin zazzafan mataki in hakan bai wakana ba.
Kakakin Hamas Osama Hamdan a ganawa da manema labaru a birnin Algiers ya maida amsa ga Trump cewa ya na tammanin zai riƙa magana cikin hikima da sa kalmomin diflomasiyya.
Isra’ila ta tura wasu matsakaitan jami’ai a mukami wajen tattaunawa da Hamas bisa jagaorancin ƙatar da Masar.
A na sa ran shugaban hukumar leƙen asirin Isra’ila wato MOSSAD Daɓid Barnea zai isa wajen ganawar.
Ba alamun za a iya cimma yarjejeniya ta kai tsaye sai dai a cigaba da samun yau fari gobe tsumma. Da dai gwamnatin Joe Biden za ta cimma nasarar a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da ta samu yin hakan a yawan ziyarar aiki da sakataren waje Anthony Blinken ya kai gaɓar ta tsakiya kan yaƙin na Gaza. Wata damuwar shi ma Trump na furta kalmomin barazana ga gefen Hamas kan sako sauran kamammun Isra’ila ba tare da dakatar da yakin ba. Abun fata a nan Trump ya yi amfani da yarjejeniyar nan ta ABRAHAM ACCORD wajen jan hankalin Isra’ila ta dakatar da yaƙin na Gaza. In za a tuna a 2020 Trump ya hada kan wasu ƙasashen Larabawa su ka dawo da diflomasiyya da Isra’ila kan cewa duk tarihin su na da alaka ko tushe daga Annabi Ibrahim Alaihis Salam.
Yaƙin Gaza ya sa duniya ta kawar da kai daga fitinar Sudan da Yukrain. Kafin shigowar Trump har ila yau gwamnatin Biden ta aza takunkumi kan shugaban mayaƙan sa kai na Sudan Hamedti Hamdan Dagalo don laifukan yaƙi.
Tun watanni 18 da su ka wuce mayaƙan sa kan ke fafatawa da sojojin ƙasar ta Sudan don gwagwarmayar karɓar madafun iko.
Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya zargi mayaƙan na sa kai da haddasa kisa ga dubban ‘yan Sudan da sanya mutum miliyan 12 rasa muhallan su.
Kazalika Amurka ta ce mayaƙan na kashe mata da yara da afkawa wasu da gangan bisa bambancin ƙabila har ma da yin fyaɗe.
A nan Amurka ta ce za ta rike duk wata dukiya da Dagalo ka iya mallaka a Amurka da haramta ma sa shiga Amurka.
Shugaban sojan Sudan Janar Abdelfatah Burhan ya yi maraba da tayin da kasar Turkiyya ta yi na sa baki don sulhunta fitinar ƙasar ta tsawon wata 20.
Sudan dai na cikin fitinar gwagwarmayar karɓar madafun iko tsakanin ɓangaren sojan ƙasar da Janar Burhan ke jagoranta da kuma rundunar sa kai da Janar Hamdan Hamedti Dagalo ke jagoranta.
Fitinar ta haddasa asarar rayuka da dukiyar jama’a da ma daidaita lamuran gwamnati a Sudan.
Burhan ya bayyana maraban ne a ganawa da mataimakin ministan wajen Turkiyya Burhanettin Duran a Port Sudan.
Janar Burhan ya ce Sudan na bukƙatar kawayen ƙasar su sa baki don warware taƙaddamar da ke addabar ƙasar.
Shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan ya ma bugawa Burhan waya don tattaunawa kan wannan manufar.
Da alamun Sudan ba ta da gata don yadda za a iya cewa kasashen duniya masu tasiri su ka bar ƙasar ta wargaje a hannun wasu tsiraru masu fafutukar samun madafun iko. A wani lokacin ma kai ka ce a na nunawa ‘yan Sudan ne cewa su je su cigaba da kashe kan su.
Kammalawa;
Yayin da za a zuba ido a ga kamun ludayin Donald Trump daga fadar White House kan fatar kawo ko rage zubar da jini a Gaza, daidaita lamura a Sham da kashe fitinar Sudan; su ma ƙasashen Larabawa na da gagarumin ƙalubalen rage biyewa siyasar duniya da kare gwamnatocin su wajen haɗa kai da kawo maslaha ga sauran dangi. Baya ga taimakon barguna da shawarwarin a tsagaita wuta ya na da muhimmanci su riƙa yamutsa gashin baki don a san da gaske za su iya cizo inan matsa mu su lamba. Wato kare ƙasashen su kadai ba zai ɗore a ƙarshe ya zama mu su alheri ba don zuba ido gobara na ci balbal a makwabta ba farar dabara ba ce don harshen wuta na neman makamashi ne kawai.
