Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A duk lokacin da aka ce kakar zaɓe ta tsaya, ’yan siyasa da masu goyon bayansu na fitowa su bayyana manufofin su da buƙatar a zaɓe su a muƙamai daban-daban. Yayin da suke alƙawura iri-iri ga jama’a don samun amincewa da goyon baya. Wani lokaci ma har da alƙawuran abubuwan da ba za su iya ba, ko kuma ya wuce ikon kujerar da suke nema, duk dai domin jan ra’ayin jama’a da masu faɗa a ji.
Gwamnoni da dama a Nijeriya suna daf da cika shekara biyu da zaɓen da aka yi musu, tare da ’yan Majalisar ƙasa da na jihohi, yayin da a wasu jihohin da aka yi zaɓen ƙananan Hukumoni shugabannin al’umma a mataki mafi kusa da talakawa, sun shafe watanni, wasu ma sun yi bikin cika kwanaki ɗari a ofisoshinsu.
Jama’a na ta murna da sauyin siyasa da aka samu a jihohin ƙasar nan, inda aka samu sauye-sauyen sabbin gwamnoni da ’yan majalisa. Mutane sun yi ta murna bisa sauyin siyasa da ya waiwayo ta kansu, ’yan uwansu, ko ’yan garinsu, ko ’yan jam’iyyarsu ne yanzu akan mulki. Yawancinsu ba suna murna don yankinsu ko jihohin su za su samu cigaba, da shan romon dimukraɗiyya ba ne, sai don wani son zuciyarsu.
Wani ɗan siyasa da aka zaɓe shi a karon farko a matsayin shugaban ƙaramar Hukuma, a wata jiha a arewacin Nijeriya yana gaya min irin yadda jama’a ke kaiwa da komowa tsakanin gida da ofishinsa, domin neman tallafi da kwaɗayin samun na cefane ko wata buƙata ta ƙashin kansu ba ta al’umma ba. Abin da yake sa ba ya iya samun zama a kusa da iyalinsa ko ya samu hutu a lokacin da ya kamata, saboda ƙwarzabar jama’a. Wasu ma da ba su samu ganinsa ba, sai dai su yi ta aikawa da saƙonnin neman taimako, da lambobin asusun ajiyarsu na banki, don a tura musu wani abu.
Waɗannan abubuwa duk sanannu ne a wajen ’yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati, waɗanda ke fakewa da irin wannan bani-banin daga jama’ar mazaɓunsu, kan dalilin kasa gudanar da ayyukan da aka zaɓe su su yi, ko kuma aikata cin hanci da rashawa, don su samu gyara siyasar su. Suna masu cewa, buƙatun jama’a gare su ne ya hana musu cimma buƙatar da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora musu. Wannan kuma a mafi yawan lokaci ba gaskiya ba ne, ɗan siyasa idan mai aiki ne hidimar jama’a ba ta hana shi yin ayyukan da aka zaɓe shi ya yi.
Na kawo wannan ne a matsayin hujja na kuskuren da jama’a da ’yan siyasa suke yi, na kasa fahimtar me ya kamata su fi mayar da hankali a kai don zaburar wakilan da suka zaɓa na siyasa, su yi musu aikin da aka zaɓe su dominsa. Wasa wasa dai ga shi muna gani lokaci na ta tafiya, amma a wajen wasu ’yan siyasar kamar yanzu aka fara. Suna ta sharholiya da bukukuwa, ba tare da sun tuna da nauyin da ke kansu ba. Sai zaɓe ya sake gabatowa sannan ka ga an tayar da ayyuka, har da waɗanda aka san ba za a iya gamawa ba, domin ya sake yaudarar talakawa a nuna musu ana samar da ayyukan raya ƙasa a yankunansu.
Ya kamata jama’a su gane don sun zaɓi mutum ba hujja ce ta jibge masa damuwoyin da suka fi ƙarfin albashinsa ko kujerar da suka ɗora shi a kai ba. Ko da yana yi musu ayyuka na kyautatawa don cin moriyar dimukraɗiyya ba shi ne ke nufin wannan ne aikin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora masa ba. Ya kamata kowacce al’umma ta kafa kwamiti na ƙwararrun mutane da za su riƙa nazari da bibiyar ayyukan da wakilansu suke yi a kowanne mataki, don tunatar da su, da kuma farkar da su kan alƙawuran da suka yi na baya. Sannan su yaba musu a inda suka nuna bajinta, hakan yana ƙara ƙarfafawa ’yan siyasa gwiwa, domin aikinsu yawanci na ganin ido ne. Suna so jama’a su ji su gani, don idan wani zaɓe ya zo su tuna wa jama’a abubuwan da suka yi.
Yanzu da aka bai wa ƙananan Hukumomi suka samu ’yancin sarrafa kuɗaɗen su, yana da muhimmanci shugabanni da Kansiloli su fitar da ayyuka na musamman da talakawa a karkara za su shaida su fahimci gwamnati na aiki. Haka kuma ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattijai da aka samar da tsarin aiki da hukumomi masu gudanar da kwangilar ayyukan raya ƙasa a madadin kuɗaɗen ayyukan raya mazaɓu da ake biyan ’yan majalisu. Yana da muhimmanci ’yan majalisar su ƙara mayar da hankali wajen ganin jama’ar su sun amfana da wannan dama.
Haka su ma gwamnoni da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati su tabbatar da sun cika alƙawuran da suka yi wa talakawa, da wanda suka shigar cikin kasafin kuɗaɗen jihohin su, domin rama wa kura aniyarta. Kuma dama masu hikimar magana na cewa, don tuwon gobe ake wanke tukunya.
