Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai ba matasan Najeriya mulki salin-alin ba sai an kai ruwa rana.
Ya ƙara da cewa ‘yan siyasa su na amfani da hanyoyin ko a mutu ko a yi rai don cin zabe.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ɗin ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya, wanda Cibiyar ‘African Centre for Leadership, Strategy and Deɓelopment’ ta shirya.
Amaechi ya jaddada buƙatar kula da harkokin siyasa, yana gargaɗin cewa dole ne a yi gwagwarmaya don samun mulki, tare da buƙatar ‘yan Nijeriya su kare ƙuri’unsu idan suna son samun jagoranci na adalci.
“Abinda ya sa Ibrahim Shekarau ya zama gwamna shi ne saboda mutane sun fito sun tsaya a layi.
“Kuna ta magana kuna zagin kowa. Babu wanda ke da mulki kuma zai ba ku— har da ni ma. Idan kuna so fasto ya zama shugaban ƙasa, ku nemo shi.
“‘ɗan siyasa a Nijeriya yana nan ne don ya yi sata, ya raunata, ya kashe domin ya cigaba da riƙe mulki. Idan kuna tunanin Tinubu zai ba ku mulki, to kuna ɓata lokacinku,” inji Amaechi.
Da yake tsokaci kan tafiyarsa na kashin kai a siyasar Nijeriya, Amaechi ya bayyana cewa talauci da larura ne ya sanya shi shiga harkar siyasa.
“Abin takaici a gare ni, talauci ya sanya ni cikin tsarin siyasa tun lokacin da na bar jami’a a 1987, kuma na kasance cikin tsarin har yau,” inji shi.
Amaechi ya ƙara da cewa shekarun da ya yi a fagen siyasa, musamman jam’iyyar All Progressives Congress, sun sanya shi zama wani babban jigo wanda ba za a iya “kore shi ba.”
