An sake zaɓar Mai’adua a matsayin shugaban NULGE na Katsina 

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta ƙasa (NULGE) reshen jihar Katsina ta sake zaɓen Nasiru Wada Mai’adua a matsayin shugabanta tare da wasu mutane 12 a karo na biyu da za su cigaba da jagorantar ƙungiyar nan da shekara 3.

Zaɓen da ya gudana a hedkwatar ƙungiyar da ke Katsina an bi ta hanyar sasantawa a tsakanin yan takara kamar yadda tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada.

A jawabin sa bayan bayan kammala zaɓen gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya sami wakilci na sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari ya tabbatar da gwamnati za ta cigaba da aiki tare da ƙungiyar domin cigaban karkara.

Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ba ƙananan hukumomi a jihar cikakken ’yancin cin gashin kansu tare da yaba wa ƙananan hukumomi bisa irin haɗin kai da suke ba gwamnatin jihar wajan aiwatar da manufofin ta.

Da yake jawabi shugaban ƙungiyar Nasiru Wada ya bayyana wasu nasarorin da ƙungiyar ta samu a tsawon mulkin.

“Nasarorin kuwa sun haɗa da tabbatar da ’ya’yan ƙungiyar sun kai matakin albashi na 16 da kuma tabbatar da ana biyan ma’aikatan albashi akan lokaci,” inji Mai’adua.

Shugaban ƙungiyar ya sanar da cewa nan bada jimawa ba ƙungiyar zaɓa buɗe shagon sayen kayan masarufi a ƙananan hukumomin 34 da ke jihar domin sauƙaƙa wa ’ya’yan ƙungiyar halin matsin rayuwa.

Sai ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta sa ’ya’yan ƙungiyar wajan rabon kayan aikin noma .

Shugaban ƙungiyar kwadago a jihar Hussaini ‘Yanduna a nasa jawabin ya yaba wa gwamntin Dikko Raɗɗa da ta fara biyan sabon tsarin albashi.

By ukarofi