Wannan bidi’a ta karɓu

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Muna yara sai ka ga ranar Alhamis ko Juma’a da safe ake ɗaurin auren ’yan mata, da daddare kuma bayan Isha ake na zawarawa. Sannu a hankali sai aka fara na Asabar da Lahadi, saboda ’yan boko a wannan ranakun ke samun hutun aiki.

A duk waɗannan ɗaure-ɗauren auren za ka samu a gidajen amarya ake zuwa karɓo aure. Wannan unguwa za ta ɗauki harami, yara su ci kwalliya da ’yan mata, a dafa abinci kaɓaki-kaɓaki.

Yan uwa da ke unguwannin nesa da na ƙauyuka ko wasu jihohi su taho duk a haɗe a yi ta murna da sada zumunci. ’Yan uwa da abokai da aka daɗe ba a sadu ba, a gaggaisa. Da yamma a yi ajo, samari da ’yan mata kowa ya shaƙata.

Ana nan sai aka fara kai ɗaurin aure a manyan masallatai, musamman na Juma’a. Limamai na samun damar karɓe kuɗaɗen sadaka, ai shi kenan aka rushe al’adar ɗaurin aure a gidaje. Ba laifi ba ne ɗaura aure a manyan masallatai, amma dai ya rushe zumunci matuƙa da aka san al’ummar Bahaushe da ita.

Abin takaicin ma shine ka na iya zuwa ɗaurin auren wani makusancinka, amma saboda cunkoso ba ka iya samun rabin minti tare da shi ba (Ko kuma ka kasa gano waɗanda ka je wa ɗaurin ma, saboda na mutane da dama akan yi a lokaci ɗaya). Da ka je kowa ka gani a irin wannan yanayi a gaggauce kuma a tare wa mutanen gari hanyoyi babu gaira babu dalili! Sannan wasu ba sa iya halarta, saboda nisa. To, ku na unguwar Kurna an kai ɗaurin aure masallacin Al-Furƙan a GRA Nasarawa.

Amma malaman da za su nuna akasin wannan tsari sun yi gum, ko don iya yawan ɗaurin auren da suka ɗaura iya yawan tsarin da za su karɓa ne? Ya kamata al’umma wani abin ta yi wa kanta magani. ƙwarai za mu iya magance wannan matsala idan muka daina rububin kai auren ’ya’yanmu zuwa masallatai, muka ɗaura abinmu a gidajenmu.

Na ga Muktar Mudi Spikin ya bada labarin yadda cikowa a ɗaurin auren wani masallaci ta sa aka ɗaura auren wasu daban da waɗanda ba su ne abokan aurensu ba. To, Ina dalili fisabilillah? To, Kowa ya koma ɗaura aure a masallacin lungunsu, ba sai an yi cincirindo a manyan masallatan Juma’a ba.

Malam Ali marubuci ne kuma manazarci daga birnin Kano

By ukarofi