Nasiha ga Musulmi da mulhidai na wannan zaure

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Allah ya saka wa waɗanda su ka ƙirƙiri wannan zaure na WhatsApp a ƙoƙarinsu na ganin an yi tattaunawa ta fahimta tsakanin waɗannan ra’ayoyi mabambanta. Shawara ta farko ga Musulmi ce, Ina son mu fahimci cewa, ta wata siga, mun fi buƙatar abokan zamanmu mulhidai fiye da ’yan uwanmu Musulmi.

Dalili kuwa shine, tantama / kokwanto (wato doubt) ita ce ginshiƙin ilimi. Daga tantama / kokwanto sai tambaya ta biyo baya, idan an dace sai a sami amsa da za ta bada waraka. Yadda Mulhidi ke kallon addini da wahala mu Musulmi mu kalle shi haka har mu iya yin tambayoyin da shi zai yi. To, ta wannan mahangar kaga Mulhidi zai azama mu izuwa nazari da bincike a kokarin lalubo masa amsa.

A duniyar yau ta Musulmi, kallon gidadawa jahilai ko ’yan taadda akasari ake yi mana, kuma akwai hujjoji ƙwarara dalilin yi mana wannan kallo. Allah ne ya umarce mu da; Q16:125 “Ka yi kira ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi Mai kyau, ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi kyau.” Wannan ne kundin tsarin wa’azi ne. A yi amfani da hikimomi (falsafa, kimiyya da duk wani ilimi), domin bada gamsashshiyar hujja.

Haƙiƙa tambayoyin mulhidai za su azama mu da ba mu ƙarƙashin nazari a bigiren ilimi fiye da wadda ’yan uwanmu Musulmi za su yi. To, sai mu yarda da tsarin girmama juna da fifita hujja, hujja ce Sarki. Su kuma mulhidai, mun sani ba wai sabon abu ba ne cewa sun kasu kashi biyu.

Akwai masu kokwanto, domin ba su sami gamsashshiyar hujja daga masu addini ba, sannan akwai jahilai ‘eɗtremists’ irin namu ’yan Boko Haram. Ba sa neman gane hujja komai girmanta, su ne Allah ya ba mu labarinsu a Q7:146 “Kuma idan sun ga dukkan aya, ba za su yi Imani ba, Kuma idan sun ga hanyar shiriya ba za su rike ta ba.” To, irin waɗannan kada ka ɓata lokacinka a kansu, domin ko me ka kawo na hujja ba ruwansu da shi sai dai izgili kawai.

Cikin mu’ujizar ƙurani ta farko ita ce “Tabat yada abi lahabin wa tab” ka ga da Abu Lahab na da hankali sai kawai ya ce ya Musulunta.

Yana Musulunta ya rushe Musulunci gaba ɗayansa saboda ya ƙaryata Allah da ƙur’ani. Amma saida ya shekara 12 bayan saukar wannan aya sannan ya mutu a kafiri. Haka ne ɗabi’ar jahilan mulhidai. Ko kuma irin su Nimrod waɗanda za su yi mujadala da kai, amma da ka kure su a hujja, sai su zama ‘violent’ (‘verbal’ ko ‘physical’), domin da Ibrahim ya ƙure shi sai ya ce a ƙona shi.

ƙalilan cikin mulhidai na iya tattaunawa da girmama mutane da sauraron hujja, to sai a tattauna da su, kuma ba lallai su yarda da hujjarka ba. Amma waɗancan ajujuwa na farko, shawara da Allah ya ba mu game da su ita ce Q28:55 “Kuma idan sun ji yasassar magana (Musulmi kenan) su kan kau da kai daga barinta kuma su kan ce (ga masu irin maganar) “Ayyukanmu su na a gare mu, Kuma ayyukanku su na a gare ku.”

Don haka irinsu (’yan gidan Abu Lahab) kada ka yi ‘wasting’ ɗin ‘energy’ ɗinka a kansu. Idan sun zage ka, ko dai ka ƙyale su ko ka rama daidai gwargwado, kamar yadda Allah ya ba mu zaɓi.

Mu na fata mulhidai da ke wannan zaure za su ci gaba da girmama wannan tsari na tattaunawa, amma zan daɗa maimaitawa cewa, ba za mu ɗauki izgilanci da zage-zage ba, domin babu wanda yake da ‘monopoly’ na ‘mischief’. Kowa ka gani zai iya aro rigar rashin kunya ya yafa.

A ƙarshe Ina fatan wannan zaure zai zaburar da matasan Musulmi wajen neman ilimi, kuma mu gane cewa dalilin da ya sa ake samun yawaitar hausawa na karɓar mulhidanci shine gazawar malamanmu, wajen iya ba su amsoshi na tambayoyinsu masu zurfi, domin malaman ba su san amsoshin ba tunda tun tali-tali an datse tunaninsu cewa, addini ba ya son tambaya kuma an rufe ƙofar ijtihadi.

Wajibi malamai su zabura ga neman ilimin falsafa da kimiyya don tunkarar ƙalubalen zamani. Idan ba mu manta ba, Annabi Ibrahim (AS) ne masanin falsafa har ma da kimiyya na farko, dubban ɗaruruwan shekaru da su ka gabata. Ya ce, da Allah Yaya yake halitta matacce zuwa rayuwa, (Q2:260), Allah ya ce ba ka yi imani ba ne? Ya ce, ya yi Imani, amma domin zuciyarsa ta natsu. Allah ya umarce shi da yin gwajin kimiyya na farko a tarihi. A falsafa kuma sanda ya karya gumaka, da aka rutsa shi me ya ce? Ku tambayi babbansu da ke rataye da gatari, domin ya zaburar da ƙwaƙwalwarsu cewa, wanda bai iya kare kansa ba, ta ina zai iya kare wani?

Ko da wani ya zo siyen gunki wajensa, sai ya ce shekararka nawa? Ya ce, 50. Sai Ibrahim (AS) ya ce, amma za ka sayi gunkin da aka sassaƙa jiya-jiya, ka bauta masa? (Ainihin falsafa kenan).

Falsafa da kimiyya wajibai ne a rayuwa, amma mu muna ƙyamatar ta, saboda wasu gidadawa sun mamaye mana addini da maida shi na ta’adda? To! ƙalubalenmu!!!

Malam Ali Sadiƙ manazarci ne a Kano

By ukarofi