Gwamnatin Katsina ta gina asibitoci da ɗakunan bada magani uku a kowacce ƙaramar hukuma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙaramar hukumar Ɓaure Alhaji Murtala Adamu Ɓaure ya sanar da haka a zantawar sa da manema labarai a Ɓaure.

Ya ce gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da gina asibiti a kowace mazaɓa a faɗin jihar amma an fara da mazaɓu uku kowace ƙaramar hukuma.

Alhaji Murtala ya ce a ƙaramar hukumar Ɓaure an gina asibiti uku kuma an gyara wasu biyar a cikin shekara biyu.

Shi kuwa shugaban ƙaramar hukumar zango Ahmed Aliyu ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta yi a fannin noma, ilimi,kiwon lafiya da tsaro a ƙaramar hukumar.

Ya bayyana cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa ta amince da gyara tare da faɗaɗa babban asibitin Ɓaure da aka ware kuɗi Naira miliyan 450 da yanzu haka aikin yaci kashi saba’in bisa ɗari.

Murtala ya ƙara da cewa gwamnati ta ware Naira miliyan 200 domin biyan diyya ga mutanen da aka karɓi filayen su da gonakin su don faɗaɗa asibitin.

Ya yi bayanin yadda ya shawo kan matsalar safarar miyagun ƙwayoyi daga waje zuwa ƙaramar hukumar wanda ya ce shi da yan sintiri da sauran jami’an tsaro suka yaƙi miyagun mutanen.

Haka kuma ƙaramar hukumar ta sayawa yan sintiri motoci guda uku da baburan hawa guda 13 domin bin lungu lungu a ƙaramar hukumar wajen gano masu sayar da ƙwayoyi a yankin.

Ƙaramar hukumar Mai’adua da tayi iyaka da jamhuriyar Nijar, shugaban ƙaramar hukumar Alhaji Mamman Salisu ya bayyana cewa mutanen su dana Nijar tamkar uwa da uba ne tun kaka da kakanni har ya zuwa yanzu.

“Muna da alaƙa na kasuwanci da aurataiyaa tsakanin mu da mutanen Nijar wanda nima tashi nayi na gani kuma har yanzu akwai wannan haɗakan”inji Mamman Salisu.

Sauran shugabannin ƙananan hukumomin Sandamu, Daura da Mai’adua duka maganan su ɗaya ne kan aikace aikace da gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar a yankin su.

Shima shugaban ƙaramar hukumar Sandamu ya bayyana cewa ƙaramar hukumar ta gyara asibitoci a garin RIgoji,Tsauya, Guduma da
Katsayel da kuma Ruwan Dutse.

By ukarofi