Mun ƙwato biliyan N20 na fanshon ma’aikatan bogi a 2024 – Shugaban ICPC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta ce, ta ƙwato sama da Naira Biliyan 20 na kuɗaɗen fansho da aka cire ba bisa ƙa’ida ba daga albashin ma’aikatan bogi a shekarar 2024.

Shugaban Hukumar ICPC, Dakta Musa Aliyu ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja, a wani taron karin kumallo da wasu ‘yan ƙungiyar Editocin Nijeriya.

Aliyu ya ce, hukumar ta kuma kama wasu mutane da suka kware wajen sanya sunayen ‘yan uwansu a cikin tsarin biyan albashin gwamnatin tarayya.

A cewarsa, yayin da ake miƙa wa masu kula da asusun fansho kuɗazen fansho na ma’aikata, ba za a iya cewa ga fanshon ma’aikatan bogi ba.

“Duk wani ragi da aka yi akan ma’aikatan bogi ba zai iya zuwa wurin kowane Mai Gudanar da Asusun Fansho ba, don haka Naira Biliyan 20 ne aka ƙwato.

“Mun sami damar ganowa tare da kwato wannan adadin kuma mun gano mutanen da ke sanya ma’aikatan bogi a cikin tsarin.

“Mun ma gano cewa wani ya sanya matarsa, dansa da kuma surukinsa a cikin lissafin albashi.

“Yaro ne zan shekara 15. Mun kama shi.

“Waɗannan wasu ƙalubale ne da muke ƙoaarin ganin mun magance.

“Ba ma so mu bar wannan ya sake faruwa,” inji shi.

Shugaban hukumar ya ci gaba da bayyana cewa hukumar ta yi nasarar hana wasu jami’an gwamnati karkatar da kimanin Naira biliyan 50 a shekarar 2023.

A yayin da yake neman goyon bayan kafafen yaza labarai domin samun nasarar aikin hukumar, ya ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta samar da dabarun yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ce hukumar na ƙoƙarin ganin ta cimma burinta, inda ya ce ba za ta boye bayanai ko yin sulhu a kan aiwatar da doka ba.

“Kamar yadda aka ba mu iko da kuma batun aiwatar da doka, za mu tabbatar da cewa mun raba ingantattun bayanai ta hanyar rahotanni, wasiƙun labarai da sanarwar manema labarai a gidan yanar gizon mu da kafofin watsa labarun.

“A shekarar da ta gabata, mun sami wani taron da muka gabatar da Tsarin Ayyuka na Dabarun 2024-2028.

“Tsarin aiwatar da dabarunmu ya yi daidai da dabarun yaki da cin hanci da rashawa na kasa.

“Koyaushe za mu kasance masu himma wajen tabbatar da cewa ba za mu bar wasu abubuwa su faru ba don kada mu bi inuwa,” inji shi.

Shugaban, duk da haka, ya ba da shawarar sake duba dokokin ƙasar don rage cin hanci da rashawa.

A cewarsa, duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa bai kamata ya amfana da hakan ba kamar yadda ake yi a wasu hukunce-hukuncen.

By ukarofi