Tinubu ya buƙaci a kyautata kulawa a makarantu bayan gobarar Zamfara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Laraba ne Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu a wata gobara da ta kama wata makarantar Islamiyya a Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara.

Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ne cikin wata sanarwa mai zauke da sa hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, mai take, ‘Shugaba Tinubu ya jajanta wa ɗaliban makarantar Islamiyya ta Zamfara, ya ce ya kamata tsaro ya zama ginshiƙi a makarantu.

Gobarar da ta tashi a makarantar Tsangaya (Makarantar Almajiri) ta yi sanadiyar mutuwar yara 17 tare da jikkata wasu ɗalibai 15.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnatin jihar da masu makarantar tare da addu’ar Allah ya ba su lafiya.

“Shugaban ya umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su ba da fifiko ga tsaron lafiyar yara a kowane lokaci kuma ya umurci hukumomin da suka dace a fannin ilimi don tabbatar da bin ka’idojin tsaro.”

A baya dai rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar Almajirai 17 da wasu 15 da suka samu munanan raunuka sakamakon mummunar gobara da ta tashi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu Dalijan, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar ranar Larabar da ta gabata, sakamakon ƙona masara da ta cinye, inda ɗaliban ke barci.

“Mun samu mummunan lamarin cewa wasu ɗaliban Almajirai sun rasa rayukansu a cikin wuta yayin da suke barci,” inji shi.

Malam Aliyu Abubakar Khalifa mai kula da Almajiran ya ce gobarar ta tashi ne da tsakar dare amma mutanen yankin ne suka kashe su.

Ya ce, “Ba zato ba tsammani na ji ihun ‘wuta, gobara!’ sai na garzaya waje na tarar da ɗalibai kusan 30 suna fafutukar tsira da rayukansu.

“Duk ƙoƙarin da ma’aikatan kashe gobara suka yi na shawo kan gobarar ya ci tura saboda ba su da kayan aiki,” inji Khalifa.

Ya bayyana cewa, ‘yan sa kai na yankin da jami’an ‘yan sanda sun haɗa kai wajen shawo kan gobarar tare da ceto wasu daga cikin ɗaliban da abin ya shafa.

A cewarsa, cikin kimanin ɗaliban Almajirai 100 da ke zauren, 17 sun kone ƙurmus, yayin da wasu 15 suka samu raunuka.

“Wannan babban rashi ne, amma mun yarda da shi a matsayin nufin Allah,” inji shi.

By ukarofi