Amurka: Ɗan majalisa ya nemi a tsige Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani ɗan majalisa mai suna AI Green daga tawagar Houston a Amurka ya sanar da batun shigar da wallafe-wallafe da ke neman a tsige Donald Trump biyo bayan kalamansa na cewa zai karɓe birnin Gaza.

Trump ya faɗi haka ne a yayin taron manema labarai da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a Fadar Shugaban ƙasar ta White House inda ya nemi Amurka ta ƙwace yankin tare da sake gina ta bayan zama braguzai sakamakon yaƙin sama da shekara ɗaya tsakanin Palestine da Isra’ila.

Trump ya kuma nemi a karkasa ƴan Gaza da suka rasa matsugunansu zuwa wasu ƙasashe a lokacin da ya ke ƙoƙarin karɓe birnin.

Lamarin da ya harzuƙa babbar jam’iyyar adawa ta Democrats da kuma wasu mambobin jam’iyyarsa ta Republican.

A yayin zaman majalisar ne a zaurenta dake White House, Green ya yi tsokaci game da musgunawa da tsangwamar wani ɓangare da Shugaba Trump ke ƙoƙarin yi a matsayinsa na mutum mafi ƙarfin iko a duniya.

Ya ce lallai lokaci ya yi da zai fara fitar da rubuce-rubuce na neman tsige Trump saboda ire-iren waɗannan munanan ayyuka na mugunta.

Wannan sai shi ne karo na huɗu da Green ke neman a tsige Trump bayan wasu lokuta uku a zangon shugabancin Trump na farko da ba su yi nasara ba, ya na mai cewa lokaci ya yi da zai sake waiwayar batun.

By Babaji