Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince ta ware wannan kuɗaɗen ne a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana a ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu a fadar shugaban ƙasar.
Haka kuma, majalisar ta FEC ta amince da kasa aikin hanyar zuwa matakai biyu don samar da ingantaccen aiki akan lokaci.
A yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron, Ministan ayyuka David Umahi ya bayyana cewa sashe na farko zai tashi daga kan iyakar babban birnin tarayya Abuja zuwa jihar Neja, wanda aka ƙara wa kilomita 5.71 kan ainahin taswirar aikin na farko inda sashe na biyu ya samu ƙarin yankuna a cikin jihar Kano, wanda ke da tsawon kilomita 17.
Umahi ya bayyana cewa a yayin gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa masu zuwa, irin su manyan titin Lokoja-Benin da Abuja-Kano, za su yi amfani da ingantattun kwalta maimakon wanda aka saba gani a kullum da ke saurin fashewa.
Ministan ya ƙara da cewa, ” a wannan karon ba zamu lamunci jan-ƙafa ko wani uziri irin na yin amfani da kayan aikin da zafin rana ka iya yi wa lahani ba, maimakon haka za mu gyara wuraren da suka lalace a baya kana mu tsaurara sanya ido sosai akan aikin.”
Gwamatin ta kuma amince da ware wani kasafin na Naira bilyan 18 don sake gina hanyar Wusasa zuwa Jos dake jihar Kaduna.
