Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya, a Numan, Jihar Adamawa.
Ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen, wanda mataimakinsa Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talata ya karanta.
Shugaba Tinubu, a yayin da ya ke bayyana dalilansa na ƙin amincewa da ƙudirin, ya bayyana, cewa, sashe na 22 na ƙudirin ya ba da ikon mallakar fili ga gwamna ba shugaban ƙasa ba kamar yadda ya kamata a dokar.
Kalu ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya kuma faɗa a cikin wasiƙar cewa, an cire batun yin digiri a cikin ƙudirin kamar yadda sashe na 25 (b) ya tanada.
A tuna cewa majalisar dai ta amince da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya Numan a Jihar Adamawa a shekarar da ta gabata inda ta miƙa shi ga Shugaban ƙasa domin amincewa.
