‘Yar Nijeriyar da ta rasa mafaka a Birtaniya sau takwas, ta yi nasara bayan shiga IPOB

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Daga ƙarshe, wata ƴar Nijeriya da ta rasa damar zama a ƙasar Birtaniya har sau takwas, ta yi nasarar samu bayan da ta amince ta shiga ƙungiyar masu fafutukar kafa yankin ƴan Biafra, wato IPOB.

Wani alƙali yi a ce matar mai mai shekaru 49, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta samu nasarar ne biyo bayan amincewa ta zama mambar IPOB.

A shekarar 2011 ne matar ta koma Britaniya inda kuma ta shiga IPOB a 2017. Kamar yadda aka sani, Gwamnatin Nijeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci, yayin da a Tarayyar Turai kuwa ba haka abin ya ke ba.

Wani Alƙalin Kotun Ƙoli na Birtaniya mai suna Gemma Loughran ya ce kasancewar matar mamba ce ta IPOB, tana tsoron musgunawa a Nijeriya wanda hakan ya sa ta cigaba da fafutukar neman mafakar.

Alƙalan Birtaniya sun tafka muhawara game da dalilin da ya sa matar ke neman mafakar, inda wasu ke ganin a saboda haka ne ta shiga IPOB, yayin da wasu kuwa suka ce akwai yiwuwar a ayyana ta a matsayin mai fafutukar ƴanci matuƙar ta koma gida, wanda kuma a dalilin haka za a yi kama ta bisa alaƙa da IPOB.

By Babaji