Gazawa sun ce ahir a bar su a kangayen su!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Al’ummar Falasɗinawa mazauna Gaza sun ƙara jajircewa don zama a yankin su na gado ko da kuwa a kan tituna da ruguzazzun kangaye za su riƙa kwana. Wannan na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar dakatar yaƙi tsakanin Hamas da Isra’ila da ya ba wa sauran jama’ar Gaza masu rabon ganin baɗi damar komawa gida musamman yankin arwacin Gaza. Rahotanni sun nuna yanda yankin ya zama tamkar inda a ka yi girgizar ƙasa da samun gawawwakin mutanen da Isra’ila ta kashe ta hanyar ruwan boma-bomai daga jiragen ta na yaƙi a tsawon wata 15 na fafatawa. Duk wanda ya ke da adalci zai fahimci Isra’ila ba ta damu da ran Bafalasɗine ba. Tamkar dai yadda a ke kisan kiyashi ko mutum ya sa hannun say a murje kiyashi ba tare da wani juyayi ba hakan ya auku kan Gazawa. Murnar su a fili ta ke yayin da su ka koma gurbin gidajen su. Mata na raha mata na guda hakanan su ka shiga yankin da ɗaukar cewa hakan nasara ce gagaruma a gare su ta yadda ya nuna zakararn da Allah ya nufa da cara ko a na mazuru a na shaho sai ya yi. Zai yi wuya a samu wani dan Gaza da ba a kashe ma sa wanii dangi na ƙud da ƙud ba amma hakan bai zama abun karya guiwa da rashin kyautata fatar wataran Falasɗinawa gaba daya za su samu ‘yanci ba. Yanda Falasɗinawa ke tarbar ‘yan uwan su da yarjejeniyar musayar fursunoni ta sa a ka sako daga gidajen yarin Isra’ila na nuna duk bayan wahala sai dadi. Sadaukar da kai na wadannan Falaasɗinawa ga samun ’yancin ƙasar su ba ya misaltuwa. A wani lokacin ma za a gani a zahiri Falasɗinawa na godiya ga Allah bayan rasa wani daga dangin su a hanyar wannan gwagwarmaya ta su. Ya zama abun karamci ga iyaki wani daga cikin su ya rasa ran sa a harkar fafutukar kwatar ’yancin Falasɗinu. Hatta magoya bayan gwamnatin Falasɗinawa da ke Ramallah ba sa iya amfani da baƙaƙen maganganu wajen aiyana ayyukan ’yan Hamas da rundunar Jahadi ta ISLAMIC JIHAD da ke aiki tare da Hamas ɗin. Ku duba fa a ɗan tsakanin yaƙin nan irin manyan mutane na Falasɗinawa da Isra’ila ta kashe kama daga shugaba Isma’il Haniyeh zuwa Yahaya Sinwar da manyan kwamandoji, amma hakan bai karya lagon Hamas ba. Abun da ya fi ban mamaki yanda du kasha ruwan tsuntsaye na boma-boman Isra’ila bai sa ta iya kwatar jama’ar ta da ke hannun Hamas a raye ko a mace ba. Lallai hakan na nuna Hamas na da tsari mai inganci na ɓoye sirri da sanin logar fafatawa ta neman ‘yanci ba ma irin fada da Yahudun Isra’ila. Hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Hamas ta tona don sadarwa da kauda bara a yaƙin sun fuskanci hare-hare da jefa boma-bomai masu tona ramuka a kasa da kisan kare dangi. Asibitoci ma duk sun fuskanci hare-hare ta sama da kasa don zargin nan ma Hamas na amfani da su wajen lamuran yaƙi. Shigar sojojin Isra’ila arewacin Gaza da kora Falasɗinawa kudanci da kara bin su kudancin da ruwan albarusai bai sa sun raurawa ba. Mutanen nan sun cancanci yabo. Gaskiya ina ganin addu’a ma daga sassan duniya daban-daban ta taimakon Falasɗinawa. Yanda Isra’ila ke amfani da ƙarfin da ya wuce kima a yaƙi da tsirarun mutane amma a ƙarshe har a ka samu saura da a ka yi yarjejeniya da su abun mamaki ga hatta ita kan ta Isra’ila. Yaƙin nan bai bar mata ba bare yara zuwa tsoffi kawai kan mai uwa da wabi Isra’ila ta riƙa yi. Duk inda a ka ga alamar taron mutane sai a jefa mu su bom da fakewa da cewa akwai motsin Hamas a wajen. Likitoci ma ba su tsira ba daga cin zalin Isra’ila. Tsananin sanyi ya yi sanadiyyar rasa ran wasu jarirai da hakan ko kaɗan bait aba zuciyar Isra’ila ta rungumi adalcin zaman lafiya ba sai ƙulle-ƙulle da ƙara yin sababi da barazanar wai sai ta murƙushe dukkan wani ɗan Hamas. Shin anya dukkan Gazawa ba ‘yan Hamas ba ne ba kuwa? Yadda na ga a na yaɗa labarin kullum a na kashe ‘yan Hamas da Isra’ila ke zayyanawa da ’yan ta’adda, ya ci a ce zuwa yau ba sauran dan ƙungiyar ko ma in akwai ya zama ya yi saranda.

Jami’an shugaban Amurka Donald Trump sun ce Trump ɗin ba ya nufin ƙaurar da Falasɗinawa daga Gaza dindindin sai dai damar sake gina yankin.

Wannan ya biyo bayan kalaman Trump na neman Falasɗinawa su fice daga Gaza a sama mu su mazauni a Masar da Jodan inda ba za a kashe su ko muzguna mu su ba.

Hakanan Trump na tunanin tura sojojin Amurka zuwa Gaza da hakan ya samu rashin amincewa daga hatta ƙawayen Amurka a tsakanin ƙasashen Larabawa.

Sakataren wajen Amurka Marco Rubio ya ce abun da Trump ya ke nufi shi ne Falasɗinawa su gusa na wani lokaci yayin da Amurka za ta taimaka da aikin share ruguzaazzun gine-gine na Gaza ala bashi in an gama su dawo.

Matsayar ta Trump har ma da nuna ƙaurar wucin gadi ce ba ta samu karɓuwa ba inda Gazawa ke ganin hanya ce ta raba su da kasar su ta gado.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yi watsi da matsayar Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na neman a kwashe Falasɗinawa a dawo da su yankin Saudiyya a kafa mu su kasa.

Hakan dama ya biyo bayan ra’ayin shugaban Amurka Donald Trump da ke neman a kwashe Falasɗinawa daga Gaza a raba su a tsakanin Jodan, ƙatar da Masar don samun walwala.

Saudiyya ta zayyana kalaman na Netanyahu da wuce gona da iri na masu tsaurin ra’ayi da su ka riƙa kashe Falasɗinawa da muzguna mu su tsawon shekaru 75.

A nan Saudiyya ta ce ba zai yiwu Falasɗinawa su bar ƙasar su ta gado ba kuma duk mai neman ƙaurar da su bai ma san yaya Falasɗinawa ke kishin ƙasar su da yadda kaunar ƙasar su ke zaune daram a zuciyar su ba.

Hakanan Saudiyya ta jaddada hanyar sulhu kawai ita ce kafa ƙasar Falasɗinawa a gefe da Isra’ila kuma kawo wannan bayani hanya ce ta kawar da hankali kan sulhun tsagaita wuta da a ka cimma.

Ma’aikatar wajen ta Saudiyya ta caccaki Isra’ila da kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a Gaza inda ta kashe da raunata fiye da Falasɗinawa 160,000 ba tare da ko nuna nadama ko tausayawa ba.

Isra’ila ta yi barazana cewa matuƙar Hamas ba ta sako dukkan kamammu ba zuwa ƙarshen makon nan to za ta dawo da yaƙi sabo fil.

Ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya yi gargaɗin cewa zuwa asabar ɗin nan ya zama wajibi Hamas ta sako dukkan Isra’ilawa da su ke rage a hannun ta tun kama su a kutsawar Hamas cikin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktobar 2023.

Katz ya ce rashin sako sauran kamammun zai sa Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙin da zai wargaza Gaza gaba daya da kuma murƙushe Hamas kakaf.

Haknan Katz ya ƙara da barazanar sabon yaƙin zai sa a cimma burin shugaba Trump na kwashe Falasɗinawa daga yankin zuwa ƙasashen makwabta kuma ‘yan uwan su kenan Larabawa.

An samu musayar dora laifi kan juna na keta alfarmar yarjejeniyar tsakanin Isra’ila da Hamas inda Masar da Katar da ke kan gaba a sulhun su ka tsaya tsam don tabbatar da ba a samu koma baya ba.

Hamas ta ce babban jami’in ta na tattaunawar sulhu ya na Masar, inda ta godewa ƙasashen Larabawa don matakin kin amincewa da kaurar da Falasɗinawa.

Masar da Jodan sun ƙarfafa matsayar cewa lallai a bar Falasɗinawa a ƙasar su yayin da a ke aikin sake gina Zirin Gaza da Isra’ila ta daidaita.

Wannan na zuwa ne bayan ganawar Sarki Abdullah na Jodan da shugaban Amurka Dobald Trump a Washington.

Sarki Abdullah da shugaban Masar Abdelfatah Alsisi sun tsaya tsayin daka don ƙin matsayar Trump da ke son ƙasashen biyu su raba Gazawa a tsakanin su inda za a yi amfani da kawar da su daga ƙasar su da sunan sake gina Gaza.

Buƙatar ta Trump ga ƙasashen biyu da ke cikin kawayen taron dangin Amurka na hade da barazanar in su ka ƙi Amurka za ta janye taimakon da ta ke yi mu su.

Masar da Jodan na samun gagarumar gudunmawar harkokin tattalin arziki daga Amurka don haka su kan zama kan gaba wajen mara baya ga muradun Amurka.

A nan ƙasashen biyu sun yi magana a siyasance ta nuna su na shirye su yi aiki da Trump amma wajen tabbatar da barin Falasɗinawa a ƙasar su in ya so a taimaka wajen kawo daidaito da zaman lafiyar yankin.

Masarta ce a wani lokaci cikin watan nan za ta karɓi baƙuncin taron ƙasashen Larabawa don tattauna lamuran Gaza.

ƙasashen biyu sun ce wannan matsaya ta su ita ce matsayar dukkan ƙasashen Larabawa.

Kammalawa;

Ba abun da ya ke kawo maslaha mai ɗorewa irin adalci. Ya dace manyan shugabannin duniya su yi adalci aƙalla ko da ma sau ɗaya kan wannan yanayi na rashin tabbas tsakanin Isra’ila da Hamas. Ba wa Falasɗinawa ‘yancin mulkar ƙasar su a gefe da ƙasar Isra’ila su zama makwabta ne zai kawo sararawar wanann fitina da ta faro tun 1948.

By ukarofi