An ƙaddamar da bincike kan zargin kashe mutum shida ‘bisa kuskure’ a Katsina

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar tsaron sojin saman Nijeriya, ta ce za ta yi bincike kan zargin cewa jirgin yaƙin soji ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a lokacin da sojojin ke bin wani gungun ‘yan bindiga a jihar Katsina.

A cikin wata sanarwa da daraktan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na shelkwatar rundunar, Air ɓice Marshal Olusola F Akinboyewa ya fitar, ya ce Rundunar ta yi matuƙar damuwa da rahotannin, kuma babban hafsan sojojin saman Nijeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ya bayar da umurnin gudanar da cikkaken bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace.

A ƙarshen mako ne rahotanni daga jihar Katsina, mai fama da matsalar ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Nijeriya, suka bayyana cewa wani jirgin sojin saman Nijeriya ya kai hari kan fararen hula, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

Sojojin Nijeriya sun yi ƙaurin suna wajen kai harin kuskure kan fararen hula a ‘yakin da suke yi da matsalar tsaro a yankunan Nijeriya.

Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar a yau Litinin, rundunar ta ce sojojin sama da ke aiki ƙarakshin dakarun Fansar Yamma sun yi nasara a harin da suka kai a tsaunin Yauni a gundumar Zakka da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina inda suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama kuma suka taimaka wajen daƙile harin da aka kai wa ‘yansanda da kuma ‘yan sinitirin jihar Katsina.

Ya kuma ce sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai da ke nuna cewa an kai wa yankin da ‘yan sandan suke hari inda aka kashe jami’ai biyu da ‘yan sintiri huɗu, kuma an samu tabbacin cewa ‘yan bindigar na boye a tsaunin Yauni da ke kusa da yankin kafin kai harin.

By ukarofi