Littafin IBB da labarun Nijeriya

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk abun da a ka rubuta shi kan takardu a ka kuma harhaɗa su waje ɗaya su ka zama littafi na iya zama abun nazari ko amfani bayan dubban shekaru. Abun lura a nan shi ne duk rubutun da ’yan adam su ka yi na bayan wahayin da Allah maɗaukakin Sarki ya yi ga Manzannin sa da hakan ke kan alluna ko a  ka adana su a rubuce kan takardu don mutane su riƙa karantawa. Duk umurnin Allah da ke cikin manyan littattafai na nan ko da kuwa ba littafi da za a iya ɗauka a karanta. Ma’ana lamari na manyan littattafai kalmomi ne na Allah da ke kiyaye kuma ba a canja su. ɗan adam ya samu ilimi har ya kan rubuta litttafi da kan zama taskar ilimi a tsawon zamunna. Baya ga rubutun littafi na koyar da ibada, tarihi ko wata sana’a kamar ilimin kimiyya, a kan rubuta littafin bayanin rayuwa ko yanda mutum ya gudanar da rayuwar sa ta aiki har ya yi ritaya. Irin wannan littafi kan ƙunshi tarihin mawallafin da kuma abubuwan alherin da ya ke ganin ya aikata da zai zo ko bayan ran sa a rika karantawa a na tunawa da shi. Ba a rasa kanbama wasu ɓangarori a irin waɗannan littattafan amma duk da haka ba amfanin kushe bayanan da mutum ya rubuta har dai za a iya wani rubutun da zai maida amsa kan wasu sassa da ke tababa a kai. Wadanda kan rubuta labarin rayuwar sa akasari tsoffin shugabanni ne na ƙasashe ko wadanda su ka riƙe wani babban muƙami. Irin waɗannan mutanen ko ma ba su yi wani rubutu ba tarihi ya na ɗauke da abubuwan da su ka aikata da musamman a ka naɗa a kan na’ura. Sani dai zai iya yiwuwa akwai wasu ɓoyayyun abubuwa da sai mai tarihin ne zai ambace don su fito fili. Bayanan kan zama tabbatar da wani abu ko fito da matsayar mawallafin kan wani abu da a ke danganta shi da shi don daidaita tarihi.

Tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce haƙiƙa marigayi Moshood Abiola ya lashe zaɓen watan Yuni na 1993 wanda gwamnatin sa ta soke.

Janar Babangida na magana ne a Abuja wajen taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa ta aiki mai taken “A journey in service” da asusun gina ɗakin karatu na IBB a Minna.

“Na ɗau alhakin duk abun da gwamnati na ta gudanar, soke zaɓen 1993 na daga abubuwan da su ka zama masu tsauri a rayuwa ta” Inji Janar Babangida bayan tabbatar da cewa Abiola ya cika dukkan sharuddan lashe zaɓen wajen yawan ƙuri’a da kuma samun adadin yankuna.

Janar Babangida ya yabawa gwamnatin tsohon shugaba Buhari don ayyana Abiola a matsayin tsohon shugaban ƙasa duk da hakan ya faru bayan rayuwar sa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da ya yi bitar littafin mai shafi 420 a gaban mahalarta da su ka haɗa da shugaba Bola Tinubu da Janar Yakubu Gowon ya kawo bayanan yanda Babangida ya kwance ɗamarar Dimka bayan kisan gilla ga Janar Murtala da kuma yadda juyin mulki ya kawo Buhari kan mulki a 1983 har sake juyin mulki a 1985 da Babangida ya hau da labarin su Janar Mamman Vatsa wanda a ka yankewa hukuncin kisa sanadiyyar shirin juyin mulki. Hakanan ya kawo lakabin Babangida da ya hada da MARADONA don yanda ba a gane matakin da zai ɗauka sai ya cimma nasara sai EVIL GENIUS da ke nuna hatsabibancin sa a aikin soja.

Janar Muhammad Barau mai ritaya ya ce ya yi aiki da Janar Babangida kuma har yau bai ga wanda ya yi ayyukan raya kasa irin sa ba “bazan iya lissafa ma ka irin ayyukan raya kasa da ya gudanar ba. Har yanzu ba wanda ya yi irin na shi amma ba mai magana ba ne”

Wasu Katsinawa ma da Babangida ya fara ƙirƙiro mu su jiha a 1987 da Akwa Ibom sun nuna ba za su manta da tarihin ba.

Babangida wanda ya ce yanzu ya na shirin cika shekaru 84 a duniya ya yi fatan ko bayan ran sa ɗakin karatun sa ya amfani jama’a wajen binciken ilimi.

An tara biliyoyin Naira a wajen taron inda Abdulsamad Rabi’u ya ba da kaso mafi tsoka na Naira biliyan 5 sai Janar Theophilus Danjuma ya biyo baya da Naira biliyan 3.

Tuni wasu sun shiga maida martani na jin daɗin yanda tsohon shugaban ya fito da bayanai da kuma masu suka cewa har yanzu tsohon shugaban na mulkin soja bai daina ɗabi’un sa na Maradon ba. Duk da dokar soja ta gayawa jini na wuce ga wanda a ka zarga da tabbatar ma sa laifin yunƙurin juyin mulki, wasu sun shiga juyayi na yadda gwamnatin ta IBB ta zartar da hukuncin kisa kan Janar Mamman Vatsa da wasu hafsoshin soja. Irin wannan ba zai rasa nasaba da kyamar hukuncin kisa don wannan dalilin ba maimakon ɗauri. Wasu kuma sun nuna inda Janar Abacha na raye zai yi bayanin ɓangaren sa kan soke zaɓen Abiola.

Wannan littafi ya zo ne daidai lokacin da hukumar ƙididdiga ta Nijeriya NBS ke bitar mizanin tattalin arziki. Fata dai ita ce gwammnatoci da matsoffin shugabanni da ke da kujera a majalisar ƙasa za su sanya ƙasa a farko fiye da muradin ƙashin kai. Shugabanni kan bayyana cewa sun yi kaza da kaza don inganta rayuwar talakawa kuma zai iya yiwuwa talakawan sun gani ko ba su gani ba wato sun amfana ko akasin haka daga manufofin gwamnati.

Mizanin ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya a rubu’in ƙarshe na shekara ta 2024 ya ƙaru da kashi 3.84 daga kashi  2.74 a 2023.

Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta saki rahoton da ya nuna sassan da ke waje da ɗanyen man fetur ne ke kan gaba wajen raya arzikin.

“Masu neman bayani kan mizanin farashi CPI sun sauke rahoton fiye sau dubu 500 a shekara 6 da ta wuce. Don haka wannan rahoto da na mizanin arziki GDP ya zama mai muhimmanci da mu ke fitarwa bisa bin ƙa’idoji na duniya,” inji shugaban hukumar ƙididdigar Prince Adeyemi Adeniran.

Alƙaluman sun nuna ɓangaren sufurin jirgin kasa, mota, sadarwa da cibiyoyin kuɗi na kan gaba wajen ƙarfin hada-hadar arziki a Nijeriya.

Babban jami’I na hukumar ta NBS Ibrahim Yakubu Tanko ya yi karin haske da nuna mizanin na GDP ya na duba dukkan hada-hada ce ta kuɗi kuma a kan sabuta shi bisa tafiyar zamani “akwai sana’o’i da a da ba mu sa su ba kamar harka na yanar gizo. Ga kuma harka ta sufurin yanar gizo kamar UBER da kasuwancin JUMI’A, waɗannan hanyoyi sun yi ƙarfi don a wasu ƙasashen ma su ne hanyoyin kasuwancin”

A nan hukumar ta NBS ta yi karin bayani kan mizanin farashin kaya CPI da wasu kafafen labaru su ka yi kuskuren fahimtar rahoton da ba wai ya na nuna saukowar farashi ba ne daga kashi 34% zuwa 28.4% amma sauya shekarar da a ke gwada lissafin tsada daga 2009 zuwa 2024 ya kawo bambancin bisa ma’anar yanzu a kan gwada ma’aunin ne daga bara inda dama kaya sun yi tsada.

ƙwararre a fannin mizanin farashi Dokta Abdullahi Jibrin ya duba amfanin mizanin tun da ba ya na nuna saukar farashi a kasuwa ba ne “idan gwamnati za ta daidaita albashi ta na amfani da wannan hauhawa ne. Babban banki kan yi amfani da alkaluman wajen karawa ko rage kuɗin ruwa. Talakawa ma kan yi amfani da ma’aunin wajen sarrafa kudin su”

NBS ta saki rahoton mizanin farashi da na tattalin arziki daidai lokacin da kayan masarufi su ka dan sauka a kasuwa wanda ke da alaƙa da shigo da abinci daga ƙetare da kuma kara darajar canjin Naira kan dalar Amurka.

Shin wannan ya jawo goyon baya ko akasin haka ga gwamnatin Tinubi mai ci? Mu shiga dandalin siyasa don gano wasu bayanai.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha yabo da caccaka a yayin da ya jagoranci  taron majalisar ƙoli na jam’iyyar sa ta APC.

Bai zama abun mamaki ba yadda masu ruwa da tsaki a taron jam’iyyar su ka kada ƙuri’ar nuna gamsuwa ga salon mulkin Tinubu da ya fara jawabi bayan hawa karaga da cire tallafin man fetur a Mayun 2023.

Nan ‘yan majalisar kolin APC ne da su ka haɗa da gwamnoni da ‘yan majalisar dattawa ke nuna da bazar Tinubu su ke rawa wato bisa ma’ana su na cin gajiyar wa’adin mulkin da ya ke kai.

APC dai wacce haɗakar jam’iyyu ce ta narke kuma ta hau karagar mulki a 2015, ta kawo ƙarshen mulkin PDP na shekaru 16 duk da wasu daga jiga-jigan jam’iyyar tsoffin ‘yan PDP ne  da ya sa wasu masu sharhi ke cewa babban canji a zahiri shi ne na alamun jam’iyya amma ba wani sauyin manufa ba.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin da ke sahun gaba a taron ya nuna kwarin guiwar Tinubu zai yi mulki wa’adi biyu na shekara 8 “in Allah ya yarda shi zai sake cin zaɓe nan gaba, saboda ka san shi lamari idan ka na da yanayi marar kyau ko rashin lafiya ka ke yi idan ka sha magani nan take sai ka ji wani abu marar daɗi daga bisani kuma sannan a warke”

Taron dai ya gudana ba tare da halartar wasu jiga-jigan jam’iyyar ba da su ka haɗa da tsohon shugaba Buhari da kuma tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kalaman sa ke nuna ya na adawa da lamuran jam’iyyar da ma gwamnatin Tinubu.

Masanin kimiyyar ƙididdiga Farfesa Sadik Umar ya nuna mamakin yadda taron ya tashi ba tare da jan hankalin shugaban kan halin da ƙasa ke ciki na ƙuncin tattalin arziki ba “shekara biyu fa sun gagara su kira mitin don su ce ga wani abu sai da ma Elrufai ya goranta mu su”.

Matasa masu kamfen ɗin jam’iyyar sun buƙaci kawo sauyin gaggawa don gudun kar a samu tangarda a kamfen din tazarce na nan gaba.

Garba A Koma Gona na daga waɗanda su ka yi wa jam’iyyar kamfen a zaɓen 2023 “su na mantawa ne laifin da PDP ta yi a loakcin Jonathan bai kama kafar/farcen wannan ba amma yaya a ka yi tallar jam’iyyar PDP”

Kammalawa;

Daga dawowa dimokraɗiyya a 1999 PDP ta fara mulki inda ‘yan adawa su ka karɓa don haka duk ɓangarorin biyun sun hau karaga, yanzu kuma a na neman ƙulla wata tafiyar ta shinkafa da wake ko za a iya samun sabon lale ko kuwa a’a.

By ukarofi