Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sanannen malamin addinin Musulunci Sheikh Dr Aminu Abdullahi Yammawa ya soki yadda ɗalibai ke zana jarrabawar JAMB kafin su sami guraben karatu a jami’o’in ƙasar nan.
Ya ce irin wannan jarrabawa yana hanawa ya’yan talakawa samun karatu a matakin jami’a.
Yammawa ya yi wannan magana ne a yayin da yake gudanar da tafsir na watan Ramadan a masallacin GRA da ke garin Katsina.
Ya bayyana cewa kuɗin zauna jarrabawar JAMB ya zama sai mai hali da zai iya biya wa yaron sa “shi ɗan talaka yana ji yana gani sai dai ya haƙura”Sheikh Yammawa ya ce.
Sheikh Aminu Yammawa ya ƙara da cewa tilasta wa yaro ya zauna jarabawar JAMB na hana mai ƙaramin ƙarfi cigaba da neman ilimin zamani a manyan makarantu a ƙasar.
Damin haka Aminu Yammawa yayi kira ga gwamnatin tarayya a soke wannan jarrabawar domin bai wa ɗalibai damar naman ilimi ba tare da saka batun kuɗi ba.
Jarrabawar JAMB na ɗaya daga cikin sharuɗɗa da dole sai ɗalibai sun cika kafin samun gurbin karatu a jami’o’in kasar.
