Tsaftar muhalli don kawar da cutar Kwalara

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Harkar lafiya a Nijeriya ta sake faɗawa cikin wani yanayi mai wuyar gaske, sakamakon ɓullar annobar kwalara, wacce aka fi kira da cutar amai da gudawa, a wasu jihohin ƙasar nan. A rahoton baya bayan nan da Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta fitar an bayyana cewa kawo yanzu jihohi 31 ne suka samu ɓullar wannan cuta a hukumance. Kusan za mu iya cewa, wannan annoba ta kama ƙasar nan bakiɗaya kenan. Saboda hatta a sauran jihohin da ba a ambata ba, ba yana nufin babu mai ɗauke da ciwon ba ne, sai dai ko hukuma ba ta san da labarin ba, ko kuma ciwon bai yi yawan da zai ɗaga hankalin hukumomi ba. 

Wannan babbar masifa ce da ta shafi ƙasa bakiɗaya, wacce bai kamata a yi mata riƙon sakainar kashi ba, kamar yadda muka saba yin hakan a wasu abubuwan mu a ƙasar nan. Kodayake, bisa ga dukkan alamu hukumomi musamman a ƙarƙashin Hukumar NCDC suna ta ɗaukar matakan gaggawa, don yaƙi da yaɗuwar cutar da samar da magunguna kyauta ga waɗanda cutar ta kama. 

Bincike ya nuna cewa, annobar ta fara ɓulla ne daga kudancin ƙasar nan a Jihar Legas, tun kimanin watanni uku da suka gabata, inda tun a lokacin aka sanar da rasuwar mutane aƙalla 5 wanda a hukumance aka tabbatar da rasuwar su ta  dalilin cutar amai da gudawa. Lamarin dai ya fara ne daga ƙauyuka da unguwannin talakawa waɗanda suke cakuɗe cikin ƙazanta da dagwalon ruwa. Cutar tana saurin yaɗuwa, musamman a wannan lokaci na saukar ruwan sama, ga shi kuma yadda mutane ke rayuwa a cakuɗe da juna ya bai wa cutar damar saurin bazuwa. 

Kawo yanzu gwamnatin Jihar Legas ta sanar da mutuwar mutane fiye da 500, yayin da alƙaluman Hukumar NCDC ke cewa a jihohi 31 an samu rahoton mutuwar mutane fiye da 1,528, kamar yadda rahoton ya nuna a lokacin haɗa wannan rubutu. 

Jihohin da wannan annoba ta fi illa dai su ne Legas, Bayelsa, Zamfara, Abiya, Kuros Riba, Bauchi, Delta, Katsina, Imo, da Nasarawa. Kodayake, jami’an lafiya a waɗannan jihohi na cewa, ana ƙoƙari don ganin an daƙile cutar daga cigaba da yaɗuwa. Sannan ana cigaba da faɗakar da jama’a, don su fahimci matakan rigakafi da kariya daga wannan cuta. 

Masana kiwon lafiya dai sun bayyana cewa, ƙwayar cutar bakteriya ce ke haifar da wannan cuta, wacce aka fi samu daga wurare masu datti da ƙazanta. Da shan ruwa ko cin abinci marar tsafta, ko wanda ba a dafa sosai ba. Haka kuma shan ‘ya’yan itatuwa ko kayan lambu da ba a wanke da ruwa mai tsafta ba, shi ma yana sanya cutar amai da gudawa. 

Cutar Kwalara ko amai da gudawa na farawa ne daga murɗawar ciki, bahaya mai ruwa, amai, da kasala, wani lokaci har da suma. Cuta ce da ke saurin ƙarar da ruwan jikin mutum, ta zagwanyar da jikinsa cikin ƙanƙanin lokaci. Idan bai samu kulawar likitoci ko ma’aikatan lafiya cikin gaggawa ba, mutum yana iya rasa ransa. 

Jami’an lafiya suna ƙara faɗakar da jama’a su kasance cikin tsafta sosai, musamman a muhallansu, a riƙa tafasa ruwa wanda ba a tabbatar da ingancinsa ba kafin a sha, idan kuma akwai sinadarin chlorine a kusa a saka a ruwan kafin a sha. Haka kuma kayan abinci da ake sarrafawa, su ma a tabbatar an kare su daga datti da ƙura ko hawan ƙudaje waɗanda ke yaɗa cututtuka cikin gaggawa. A riƙa dafa abinci ya nuna sosai, sannan a wanke hannu da kyau kafin a ci da bayan an gama. Kada a manta a koyawa yara su ma su fahimci illar cin abu marar tsafta, da yawan wanke hannu bayan wasa kafin a ci abinci, da bayan fitowa daga bayangida. Iyalai su riƙa adana magungunan ciwon ciki da masu tsayar da gudawa a gida, don samar da rigakafin farko tun kafin a je asibiti. Kar a manta da dabarun da malaman lafiya ke koyarwa na haɗa ruwan gishiri da suga, ko a sayo na kamfani, don kula da tsaftarsa. 

Ya kamata ma’aikatan lafiya su samar da wani tsari na faɗakar da jama’a ta kafafen watsa labarai, ta wuraren ibada kamar faɗakarwa a masallatai da majami’u, da kuma ta shiga gida-gida, don wayar da kan mata, har ma da makarantu inda yara suke a ilimantar da su da malamansu, don su ƙara sa ido kan lamarin tsafta a makaranta. Su ma jami’an dubagari da ke ƙarƙashin hukumar kula da muhalli a wasu jihohin, ya kamata su ƙara tsananta yadda suke aikinsu, ta hanyar bin mutane har cikin gidajensu ana gargaɗinsu kan muhimmancin tsafta da kula da lafiyarsu.

Sannan ina so in bai wa gwamnati shawara, kada a taƙaita wannan tallafin kula da masu lalurar amai da gudawa kyauta da aka ce ana yi, ya tsaya ga asibitocin gwamnati kawai. A tabbatar da an isar da waɗannan magunguna ga asibitoci masu zaman kansu, da ƙananan asibitoci a cikin anguwanni da ƙauyuka, don nan ne jama’a suka fi gaggawar zuwa, da zarar sun samu wannan lalura, a matsayin matakin farko. Kuma lura da halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa da talauci da ke damun jama’a da dama, ya kamata a tausayawa jama’a, kada a bari rashin kuɗi ya hana wasu zuwa asibiti, ko ya ƙara yawan adadin masu rasa ransu a dalilin amai da gudawa.

Wata matsala kuma da ita ma ke taimakawa wajen yaɗa cututtuka, ita ce yin bahaya a waje, kamar yadda ake samun wasu da ba sa son yin bahaya a gidajensu, ko kuma akwai ɗin, amma wasu sun fi son su je bayangari, ko tsugunawa a bola da wuraren wucewar ruwa. Wannan al’ada tana taimakawa wajen yaɗa cututtuka da lalata muhalli, musamman a wannan lokaci na damina, ruwa na kora wannan bahaya har ya gangara ya shiga ruwan da jama’a ke amfani da shi. Sannan ƙudaje ma na iya hawa kai su ɗauki cuta su shiga gidajen mutane su yaɗa a kan abincinsu da kwanuka, kuma a dalilin haka za a iya samun ɓarkewar amai da gudawa.

An ce rigakafi ya fi magani. Kuma kula da kaya ya fi ban cigiya. Taya Allah kiwo, ya fi Allah na nan. Kada mu zama masu sakaci da lafiyarmu da ta iyalinmu. Mu tashi tsare don ganin mun yi abin da ya kamata, da biyayya ga faɗakarwar da malaman lafiya ke yi. Sai kuma mu yi addu’a, mu bar wa Allah Ya yi nasa ikon.

Allah Ya kawo mana sauƙin wannan annoba. Ya bai wa masu jinya lafiya. Mu kuma da ba mu kamu ba, Allah ya ƙara mana lafiya bakiɗaya. Amin.

By ukarofi