
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Matasan Arewa ta AYCF, ta ƙaryata kalaman da Honorabul Aminu Sani Jaji ya yi, inda ta ce hakan wani yunƙuri ne na yin rufa-rufa ga harkokin siyasarsa mai cike da alamomin tambaya.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yerima Shettima ya ce, take-taken Jaji salo ne na cika burinsa a siyasa duk da cewa ya bar baya da ƙura domin akwai zarge-zargen almundahana da sauya aƙalar kuɗaɗe a harkokin jagorancinsa.
Shettima ya hasato zamanin Buhari, a lokacin da Jaji ya jagoranci yi wa Buhari kamfen, inda ya ce daga baya ya koma amfani da damar hakan wajen azurta kansa da sunan yaƙin neman zaɓen Buhari.
Ya ƙalubalanci Jaji da cewa, mai irin halinsa a siyasa, ba wanda zai wakilci mutane bane da muradunsu, ya na mai cewa ƴan Nijeriya suna buƙatar jagorori masu tsare gaskiya da adalci a yayin shugabanci.
Ƙungiyar ta kuma koka kan yadda Jaji ya gabatar da jawabi ga manema labarai a Jihar Kaduna a madadin Gusau inda nan ne garinsa, wanda hakan wani salo ne na ƙara samar da rabuwar kai acikin Jam’iyyar APC.
AYCF ta yi kira ga shugabancin APC da ya yi nazari game da take-taken Hon. Jaji da ɗaukar matakin da ya dace.
Har’ilayau, ƙungiyar ta jaddada aniyarta ta cigaba da ƙoƙarin kira ga samar da gaskiya da adalci acikin harkar siyasa a Nijeriya.
