Ƙananan hukumomi: NLC ta buƙaci Tinubu da gwamnoni su mutunta hukuncin Kotun ƙoli

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da gwamnonin jihohi da kada su yi siyasa da aiwatar da hukuncin Kotun ƙoli da ta umarci ƙananan hukumomi su buɗe asusu a Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin karɓar kason su kai tsaye.

Da yake jawabi a wajen taron majalisar gudanarwa ta ƙasa karo na 8 na ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) a Abuja, shugaban ƙungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya ce NLC za ta marawa NULGE baya domin ganin an samu cin gashin kan ƙananan hukumai baki ɗaya.

“Mun samu ‘yancin cin gashin kai a yanzu, ina roƙon gwamnatin tarayya da kada ta yi siyasa da ’yancin cin gashin kan da muka samu, bai kamata a saki kuɗaɗen ƙananan hukumomi ta wata hanya ba.

“A lokacin da ɓangaren shari’a na gwamnati, kotun koli a ƙasar ta yanke wannan hukunci, ba su ƙara yiwa kowa wani alheri ba, kuma har shugaban ƙasa ya yarda da hakan.

“Don haka ban fahimci jinkirin da suke yi ba, don haka NLC, NULGE da duk ƙungiyoyin kwadago a Nijeriya za su haɗa kai da dukkan ku don ganin mun yaƙi duk wani abu da ya saɓa wa doka, ko ƙananan hukumomi, ko jiha, fafutukarmu ta yi fice ta yadda ba za ta zama hanyar faɗa musu ba, ku bi doka.

“Ba tada zaune tsaye ba ne, wannan wata hanya ce ta tabbatar da doka, wadda aka shigar da ita bisa son rai, ba mu da tausayin wani gwamna, ba ma jin tausayin wani shugaban ƙasa, ba ma jin tausayin kowane minista.

“Don haka, a yau, a madadin ƙungiyar ƙwadago da NULGE da ke zama ɗaya daga cikin ‘yan majalisa masu ƙarfi, mu ce ba za mu kai shi ga wata ƙaramar hukuma ba, zuwa kowace jiha, inda wannan batu na cin gashin kansa ba a aiwatar da shi yadda ya kamata ba.

“Idan wa’adin ku ya ƙƙre, ku miƙa mulki, babu buƙatar yin maguɗi don ci gaba da zama a ofis har abada.”

By ukarofi