
Daga BELLO A. BABAJI
Wata ƙungiyar NGO a Kano da ke shirye-shiryen samar da jagoranci na gari, ta soki Gwamnatin jihar da Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin su da ƙin yin biyayya ga hukuncin doka da kuma zaman lafiyar al’umma.
A wata takarda da ta fitar a Kano, ranar Litinin, ƙungiyar ta ce da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin duk sun yi buris da umarnin ƴan sanda na hana hawan sallah a Kano a yayin bukukuwan Sallah.
Tun farko, rundunar ƴan sanda jihar ta fitar da sanarwar hana yin bikin hawan sallah da aka saba yi a kowace shekara sakamakon samun rahoton sirri da ke nuna yiwuwar samun tashin-tashina.
NGO’n ta ce, sakamakon ƙin bin umarnin da ɓangarori biyun suka yi, an samu asarar rayuka da kuma raunata da wasu suka yi a yayin wasan tseren doki a jihar.
Lamarin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin cin mutuncin mulki da kuma gazawa wajen kiyaye doka daga waɗanda ke jagorantar al’umma.
Don haka ne ta ke kira ga hukumomin tsaro da su kama waɗanda ke da alhaki da kuma gurfanar da Sarki Sanusi bisa tuhumar sa kan waɗanda aka rasa da waɗanda suka samu raunuka.
Kazalika, ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da ƙoƙarin kiyaye doka da oda da kuma tabbatar da jagororinsu sun kiyaye gaskiya da adalci.
