Cikin girmamawa da kuma nuna kishin ƙasa, da son a kawo gyara ga hukumar tsaro ta jami’an ‘yan sanda nake rubuta wannan wasiƙa.
Aikin samar da tsaro al’amari ne mai matuƙar muhimmanci a kowacce aasa, kuma musamman ma aikin ɗan sanda. ɗan sanda shi ne jami’in tsaro na farko da ke da alhakin ganin al’umma sun zauna lafiya, cikin kariya da mutuntawar samun kyakkyawar kulawa ga fararen hula. Shi yasa aikin jami’in ɗan sanda ya ta’alaƙa a kan kare rayuka da dukiyar al’umma.
Yana da kyau hukumar ‘yan sanda ta nuna wa jama’a tausayawa da kuma mutuntawa, saɓanin yadda a wasu lokutan ake samun akasin hakan.
Rashin yin aiki a doron doka da wasu jami’an ‘yan sanda ke yi a kan fararen hula, shi ne babbar matsalar da ta haifar da kallon kura da fatar akuya da mutane ke yiwa jami’an ‘yan sanda a Nijeriya.
A dokar ƙasa, aikin ɗan sanda shi ne hana aikata laifi ga farar hula wato (Ciɓilian), ba wai ya laɓe tare da zuba ido ya jira ayi laifin ba sannan ya zo ya yi kame. Kuma idan hakan ta faru ya kama wanda ya yi laifin, sai kuma ya nemi cin hanci daga gare shi don ya ƙyale shi ya tafi. Wannan babban kuskure ne, kuma ya kamata a kawo ƙarshen wannan a hukumar ‘yan sanda.
Sannan idan ɗan sanda ya kama mai laifi, za ka ga wasu lokutan shi da kansa yake nuna ayi masa wani abu ya saki mai laifin, ko kuma idan aka kawo ƙara sai a nemi wani abu a wurin wanda ya kawo ƙarar da sunan za a yi masa aiki tun kafin a biya masa buƙatarsa. Haka nan wasu lokutan idan kaga ana saurin zuwa a kamo wanda aka yi ƙara, to an ji batun kuɗi ne (wato inda za a samu kuɗi, ko kuma wani batu da ke da girma da mutum zai shiga uku ya yi asarar kuɗi idan ya zo hannunsu.
Sau da dama idan aka duba a kaga ƙarar da aka kawo ba wadda za a samu wani abu mai maiƙo ba ce, sai a ce aje gida ayi sulhu, ko a koma wajen Mai Unguwa. Wasu lokutan jami’an ‘yan sanda kan wuce makaɗi da rawa wajen yin binciken mai laifi, ko kuma rashin yin adalci da gudanar da sahihin bincike a kan mai laifi (suspect) da aka kawo musu ko suka je suka taho da shi.
ɗan sanda kan lallaɓa mutum a lokacin da yaje tahowa da shi, amma da zarar an zo chaji ofis sai ya ƙarawa wuta fetur, musamman idan wanda aka je kamowar ya ɗan nuna tirjiya kafin azo chaji ofis. To me yasa haka? Koda mutum ya nuna tirjiya in dai an riga an zo da shi caji ofis, to a rabu da batun tirjiyar da ya nuna mana kawai a tafi kan bincike ba tare da ɓata lokaci ba.
Me Ya Sa Mutanen Gari Suke Yi Wa ‘Yan Sanda Kallon Macuta?
A wasu lokutan ‘yan sanda kan yi wani abu da za a iya kiransa da wuce makaɗi da rawa. Abin da bai kai na ayi wa mutum uƙuba ba sai suyi wa mutum uƙubar da ta wuce misali, ko kuma a ɗauki laifin wani a ɗora kan wani, mutum yana ji yana gani dole ya amsa laifin da ba nasa ba, kuma hakan yafi faruwa ga waɗanda basu da galihu a cikin al’umma.
A doka an ce kada a tsare mutum yayi 24 Hours a cikin (cell) ba tare da an kai shi kotu ba, amma wani sai ya shafe sati guda tsare a wajen ‘yan sanda. Haka nan maganar beli kyauta, wannan kam a iya jikin allon chaji ofis ko bango ne kaɗai yake aiki, idan kazo belin mutum sai ka bayar da wani abu. Wani abun haushi da takaici, idan ka kawo ƙara ma sai ace ka kawo kuɗi a zuba mai a mota aje a taho da mai laifi.
A wasu lokutan jami’an ‘yan sanda kan sauya magana a kan wanda aka yi ƙara ko mai laifi, ba don komai ba sai don kawai a yi duk yadda za a yi a tatsi mutum kuɗi. Waɗannan dalilai ne daga cikin abubuwan da suka jawo mutane suke yi wa jami’an ‘yan sanda kallon kura kya ci da gashi.
Idan muka koma kan hanyoyi wato titunan motoci, za a ga jami’an ‘yan sanda suna tare motoci suna karɓar kuɗi, wanda hakan ya saɓa wa dokar ƙasa, wasu ma idan ba a basu ba sai su ajiye mutum, ko kuma su sauke kowa a mota suyi ta bincike, daga ƙarshe ba za su samu wani kayan laifi ba, ga shi sun ɓatawa direba da fasinja lokaci, kuma duk da hakan ba za su bar direban haka ba sai sun karɓi wani abu a hannunsa.
Duk wanda yake bin manyan hanyoyi ya san wannan, hatta da hanyoyin cikin gari, bakin kasuwa da wasu wuraren hada-hadar jama’a na cinikayya, za ka samu jami’an ‘yan sanda suna haza cuwa-cuwarsu. Wannan na ɗaya daga cikin abinda ya zubar da kimar ‘yan sanda, domin ba iya wannan ba ma, hatta cikin unguwannin masu kuɗi sukan shiga da mota suje gidan attajiri ko ɗan siyasa su yi parking suna neman ganin Alhaji ko Honourable don kawai su sami kuɗi. Menene wannan ban da zubar da kima da mutuncin aikin ɗan sanda?
Duk wani jami’an tsaro yana da albashi da kuma alawus da ake bashi don ya ci abinci a kullum, idan alawus ɗin baya zuwa hannunsu a wajen wa ya dace su nemi haƙƙinsu? A wajen talakawan gari da ya kamata su kare su, ko kuwa a wajen Gwamnati? Aikin ɗan sanda dai aiki ne na samar da tsaro da kuma kwanciyar hankali ga al’umma.
A kare rayukansu da dukiyarsu, a hana su aikata laifi. To amma mu jami’an ‘yan sandan ƙasarmu nema suke yi ma ayi laifin don su sami kuɗi.
Idan ire-iren waɗannan abubuwa da nake lissafowa a hukumar ‘yan sandan ba a san suna faruwa ba, to ina kira da ayi bincike a kai, musamman majalisar dokokin ƙasa. Saboda yadda aikin jami’in ‘yan sanda ya samu tasgaro, hatta abokinka ɗan sanda idan ka jero da shi kuna tafiya, to mutane za suyi ta kallon ku ne, har ka ji ana tambayar me wane ya yi? Dalili, don kawai an ganka tare da jami’in ɗan sanda.
Wata rana na dawo daga tafiya, sai muka zo wajen wasu jami’an ‘yan sanda suka tare mu suka sa direba yayi parking. Bayan mun tsaya suka ce duk mu fito daga motar a nan take muka bi umarninsu. Muna fitowa sai suka tambaye mu daga inda muka fito da kuma inda zamu je muka faɗa musu. Daga nan sai suka ware wasu mutum biyu suka caje su, basu same su da kayan laifi sai kuɗin da ke jikinsu. Nan take ganin kuɗi a wajen bayin Allah nan suka ce kowa sai ya ajiye wani abu a cikin mota, kuma haka kawai ba laifi suka yi ba. Yanzu don Allah duk jami’in da zai yiwa farar hula haka, to da wanne matsayi zai kalle shi banda mugu azzalumi? Akwai wani waje da muka zo ‘yan sanda suka tsaida mu, direbanmu ya ce musu sai ya dawo sai basu na horo, sai wani ɗan sanda ya ce, “Jiranka za mu yi har sai ka dawo, ka bamu kawai…” Ku ji wannan abu fa sai kace bin bashi.
A dalilin ire-iren waɗannan abubuwa ne da wasu jami’an ‘yan sanda suke yi yasa mutane basa jin tsoron aikata laifi kowanne iri ne, domin sun yi imanin cewa duk abinda suka aikata ko an kama su da wannan laifin dai ƙarshen maganar kuɗi ne, da zarar sun saki kuɗi ga jami’an za a sake su. Roƙo da maula ko neman abu da kamar ƙwace da wasu jami’an ‘yan sanda suke yi, abu ne marar kyau da ya kamata hukumar ‘yan sanda ta ɗauki mataki.
Idan har da gaske ana son raba mutane da aikata miyagun Laifuka a cikin al’umma da ƙasa baki ɗaya, to ya dace a gyara aikin ‘yan sanda. Su tsaya su yi aiki bisa kishin ƙasa da amana, wallahi duk jami’in ɗan sandan da yake karɓar cin hanci to ba mai kishin ƙasa ba ne. Kuma muddin za a ci gaba da yi wa mutane bita-da-ƙulli a hukumar ‘yan sanda, to masu aikata laifi za su ci gaba da ƙaruwa ba adadi. Amma idan aka gyara aikin ɗan sanda, a ka daina karɓar cin hanci, da kuɗin beli, da ɓoye gaskiya a yayin binciken laifuka, to ƙasa zata ci gaba da haifar da rashin zaman lafiya.
Ko shakka babu, adalci shi ne abinda yake kawo zaman lafiya. Na zaɓi yin wannan rubutun rubutacciyar wasiƙar ga jami’an ‘yan sanda ne saboda ina jin babu daɗi ga abinda wasu a cikin hukumar ke yi da sunan aikin ɗan sanda. Muna ganin yadda ake yin aikin ɗan sanda a ƙasashen duniya, wanda wallahi ya sha bamban da namu jami’an ‘yan sandan. Don haka ya kamata a gyara domin al’ummar ƙasa suyi alfahari da jami’an ‘yan sanda, a daina yi musu kallon azzalumai macuta.
Idan ‘yan sanda suka tsayu a kan aikinsu da adalci, to babu wanda zai raina su balle yayi musu kallon masu cuta a cikin al’umma. Haka nan idan ‘yan sandan ƙasarmu suka ƙauracewa gidajen ‘yan siyasa ko ofisoshin su da sunan zuwa neman na goro, to babu wani ɗan siyasar da zai juya su. Kamar yadda ake zargin su a yanzu, ana ganin cewa sun zama karnukan farautar ‘yan siyasa, suna musu aiki a ɓoye da fili. Haka nan kuma ‘yan siyasa kan yi amfani dasu wajen cikar muradunsu.
Ina fatan abubuwan da na faɗa su zamo abin duba na tsanaki ga hukumar ‘yan sanda don magance duk wata matsala da zata jawo zubewar kima da mutuncin ɗan sanda.
Daga NAFIU SALISU. Marubuci. [email protected]@gmail.com.08038981211, 09056507471.
