EFCC ta cafke Aisha Achimugu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Jami’an hukumar EFCC sun kama mashahuriyar ‘yar kasuwa kuma fitacciyar mace a fagen zamantakewa, Aisha Sulaiman Achimugu, da safiyar Talata.

Lauyoyinta ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau Talata, inda suka ce Achimugu ta dawo Najeriya daga birnin London da kanta, kuma aka kama ta da misalin ƙarfe 5 na safe.

A cewar rahotanni, lauya da ke kareta ya shaidawa babbar kotun tarayya dake Abuja cewa ta riga ta bayyana a cikin takardun kotu cewa za ta kai kanta ofishin EFCC a yau Talata, domin amsa tambayoyi kan wani bincike da hukumar ke yi na zargin haɗa baki wajen aikata laifi da kuma wanke kuɗaɗe.

A ranar Litinin da ta gabata, mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umurci Aisha da ta bayyana gaban EFCC a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025, domin amsa tambayoyi da suka shafi zargin aikata laifi.

Kotun ta kuma umurce ta da ta bayyana a gabanta a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, 2025, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

By ukarofi