Hajjin 2025: Tawagar jami’an NAHCON ta je Makkah domin sharar fage

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya, NAHCON, ta fara gudanar da harkokin aikin hajjin bana biyo bayan tura tawagar jami’anta na farko zuwa ƙasa mai tsarki a Saudiyya.

Babban jami’in labaranta, Shafi’i Mohammed ya faɗi hakan a wata sanarwa, ranar Litinin, inda ya ce manyan jami’an gudanarwa da na tawagar kiwon lafiya ne suka tafi Makkah daga Abuja a ranar.

Daraktan hukumar gudanarwar NAHCON, Alhaji Babagana Bukar ya yaba wa ƙoƙarin jami’an bisa salon sauke ayyukansu na hajjin bara, inda ya kuma jaddada yarda da su a matsayin waɗanda za su kula da harkokin aikin hajjin yadda ya kamata.

Ya kuma yi kira ga shugabancin hukumar ƙarƙarshin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, da su cigaba da ba su goyon baya don cimma nasarori a yayin aikin hajjin.

A nasa jawabin, Farfesa Abdullahi Saleh, ya yi kira ga mambobin tawagar da su riƙe gaskiya da adalci a yayin sauke nauyin da aka ɗora masu.

Ya kuma ce, lallai akwai buƙatar a samu haɗin kai a tsakaninsu wajen yin kama-kama don tabbatar da cika aiki, lamarin ka iya zama nasara a gare su da ma hukumar baki ɗaya.

Kazalika, ya tabbatar masu da samun cikakken goyon bayan NAHCON gami da tunatar da su tsoron Allah a yayin ayyukansu.

By Babaji