
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Gudaji Kazaure, ya shiga hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC, bisa zargin sa da karɓar Naira miliyan 70 daga hannun tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an hukumar sun kama Gudaji ne jim-kaɗan bayan bayan wata babbar kotu a Kano ta soke umarnin hana kama shi.
Wata majiya a EFCC ta ce, Kazaure ya karɓi miliyan N20 daga hannun wani ɗan aiken Emefiele domin sayen ragunan Sallah.
Daga bisani Emefiele ya ba shi miliyan N50 sakamakon aukuwar gobara a gidan tsohon ɗan majalisar.
Ya kuma ce, an tsare Gudaji ne a ofishin hukumar dake Kano, inda daga bisani ake sa ran kawo shi Abuja domin gurfanar da shi.
A watan Disambar 2022 ne Gudaji ya zargi Emefiele da hannu a rashawa da ya ƙunshi batun ɓatar da Naira tiriliyan 89.1 na kuɗin cajis da ake kira da ‘Stamp Duty’ a lokacin da ya ke gwamnan babban bankin.
Saidai, Fadar shugaban ƙasa ta hannun Kakakin gwamnatin wancan lokacin, Garba Shehu, ta ƙaryata zargin Kazaure, kuma ya ce tun a lokacin aka rushe kwamitin da aka kafa game da bincike akan lamarin.
