Trump a Riyadh kan Gaza?

Spread the love

Me ma mutum zai ce ne in ka na bin siyasar duniya ba za ta tantance barcin makaho ba da farkawar sa musamman ta ɓangaren adalci. Shin karyawa da ziyara gabar ta tsakiya a wannan dawowa ta Trump kan ragama na nuna fifita yankin ne ko dai akwai wasu ɓoyayyun lamura. A wancan mulkin na sa ma ai ya shigo Saudiyya daidai lokacin da wasu da ke caccakar Saudiyya ke ganin hawan sa madafun iko ma tamkar babbar barazana ce ga sarakunan na Saudiyya. Shiga Saudiyya a matsayin madakatar farko ta shugaban na Amurka na nuna matsayin Saudiyya a tsakanin ƙasashen yamma na irin tasirin da ta ke da shi a tsakanin Larabawa, ƙasashen Musulmi, galaba kan man fetur da sauran su. Shin kun tuna yadda kashe ɗan jarida Jamal Kashoggi a Istanbul ya sha ruwa bayan Turkiyya ta fidda shaidar cewa Saudiyya ce ta aikata hakan a ƙaramin ofishin jakadancin ta a Turkiyar? Gaskiya ne kashe Kashoggi ta hanya mai ban tausayi da daddatsa naman jikin sa ya sa wasu na tunanin Amurka ƙarƙashin Trump za ta ƙullaci Saudiyya da akalla ma yanke hulɗar jakadanci ko ma aza ma takunkumi. Duk maimakon hakan ma alaƙa ce ta ƙara yauƙi tsakanin ƙasashen biyu inda Trump ya zayyana kashe Kashoggi da wani lamari da ya shafi cikin gida na Saudiyya. Tona asirin abun da ya faru ya sa hukumomin Saudiyya nuna ɗaukar mataki kan wasu jami’an ayyukan sirri na ƙasar ko ma a ce ɗora mu su alhakin aikata haka maimakon ya zama mataki ne na hukumomi ko shugabannin Riyadh. Hakanan Yarima Muhammad bin Salman ya yi alheri ga iyalan Kashoggi da nuna za a yi adalci ga akasin da a ka samu. Kasancewar an bada labarin hilatar Kashoggi ya taho Istanbul da tsohon jakadan Saudiyya a Amurka Yarima Khalid wanda ƙanin Yarima Muhammad ne, sai alamu su ka nuna an ɗauke shi daga harkokin diflomsiyya an dawo da shi gida da samun gagarumin muƙami na ministan tsaro kuma na’ibi na biyu mai jiran sarautar Saudiyya. Wannan ya nuna bias tsarin in Allah ya yi wa Sarki Salman rasuwa, Yarima Muhammad matashi zai hau sarauta inda Yarima Khalid zai zama na’ibi na ɗaya mai jiran gado. Yanzu dai ba wannan fage na ke son faɗaɗawa ba ina son duba labarun ziyarar Trump ne birnin Riyadh da duk fitattun lamuran tsaron duniya da ke dangantaka da hakan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya maimaita kira ga shugaban Rasha ɓladimir Putin da na Yukrain ɓolodymyr Zelensky su dakatar da yaƙin da su ke yi.

Trump na amsa tambaya ne a fadar White House gabanin tafiyar da ya daura zuwa Saudiyya, Katar da Daular Larabawa.

Wannan na zuwa ne bayan ofishin jakadancin Amurka a Kyiɓ ya fidda gargadin shirin kawo hare-haren boma-bomai kan Yukrain daga Rasha.

Trump ya buƙaci shugabannin biyu su dakatar da yaƙin da ya zaiyana marar amfani su kuma dawo batun tsagaita wuta na tsawon kwana 30.

Donald Trump ya bugi kirjin kawo ƙarshen yaƙin mamaye Yukrain da Rasha ta ɗaura bayan Yukrain ɗin ta aiyana neman shiga ƙungiyar tsaro ta Turai wato NATO.

Za a jira a ga ko buƙatar ta Trump za ta biya yayin da alamu ke nuna Rasha ba ta son ɗaukar wargi daga Yukrain.

TRUMP YA SAUKA A RIYADH

Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a birnin Riyadh na Saudiyya a matsayin ziyarar aiki ta farko ƙetare bayan dawowar sa madafun ikon White House a karo na biyu amma ba a jere ba.

Yarima Muhammad bin Salman ya tarbe shi a filin jirgi don shirya tattaunawa ta musamman.

Haƙiƙa lamarin buƙatar tsagaita wuta a Gaza ne kan gaba a tattaunawa da Trump wanda kazalika zai shiga Katar da Daular Larabawa kuma ta yiwu ya bi ta Turkiyya don tattaunawa kan batun yaƙin Yukrain.

Daidai tahowar Trump, Hamas ta sake Ba’Isra’ilen Ba’Amerke Edan Aleɗander da ke cikin sauran kamammun da ke hannun Hamas.

Trump ya baiyana farin ciki da sako Aleɗander da ya ce zai koma gida bayan iyalin sa sun ɗauka ya mutu.

Trump wanda ya yi sanyi kan neman sulhun Gaza ya yi alwashi a baya cewa zai kawo ƙarshen fitinar nan take amma wankin hula ya kai dare .

Ziyarar ta Trump gabar ta tsakiya za ta kuma tabo tattaunawa kan batun makaman kare dangi na Iran.

Isowar Trump ke da wuya sai ƙasar Saudiyya ta rantaba hannu kan yarjeniyoyin hulɗa da sauran lamuran raya arziki da su ka kai darajar dala biliyan 300 da Amurka.

Donald Trump ya yi farin ciki da wannan nasarar ƙarfafa hulɗar arziki inda ya jinjinawa Yarima Muhammad da nuna shugaba ne abun alfahari.

In za a tuna ko a mulkin Trump na farko Yarima Muhammad ya kai ziyara farar White House inda ya rantaba hannu kan yrajeniyoyin arziki kwatankwaci ko ma fiye da abun da su ka ƙulla a wannan karo.

Amurka ta baiyana shirin janye dukkan takunkumi da ta azawa ƙasar Sham wato Siriya don ba wa ƙasar damar numfasawa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana haka a taron cibiyar kasuwanci a birnin Riyadh ɗin Saudiyya.

Bayyana aniyar dage takunkumin ya sa mahalarta taron tashi da yin sowar yabo ga Trump inda shi kuma ya nuna jin daɗin cewa kamar ya ba wa Yarima Muhammad wani tukuici ne.

Trump ya nuna fatar Sham za ta samu cigaba don sabuwar gwamnatin da a ka samu, ya ƙara da cewa ya dau matakin dage takunkumin bayan tattaunawa da Yarima Muhammad da kuma shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan.

A nan za a yi fatar Isra’ila za ta rage hare-hare da ta ke kai wa cikin Sham da sunan farautar mayaƙan Iran ko gyauron Hezbollah da ke ƙasar da su ka shiga don taimakawa tsohon shugaba Bashar Al’Asad kan mayaƙan da a yanzu su ka amshe madafun iko.

Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci lallai Iran ta dakatar da abun da ya zaiyana da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin mayaka ko yaƙi ta hannun ƙungiyoyi mayaƙa.

Amurka na zargin Iran da amfani da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon da Houthi a Yaman wajen yin yaƙi don kare muradun ta.

Trump na Magana ne a taron ƙungiyar haɗin kan shugabannin gabar ta tsakiya da a ka gudanar a Riyadh.

Donald Trump na nuna dakatar da amfani da ƙungiyoyin mayaƙa ya zama cikin yarjejeniyar dakatar da batun kera makaman ƙare dangi na Iran da ya sa Amurka azawa Iran ɗin takunkunmi daban-daban.

A nan shugaban na Amurka ya nemi shugabannin ƙasashen na gabar ta tsakiya su matsawa Iran ta daina yaƙin bagaye ta hanyar ƙungiyoyin mayaka.

A shekarar nan kaɗai an samu tattaunawa kimanin sau hudu tsakanin Amurka da Iran kan batun dakatar da kera makaman na ƙare dangi.

Trump ya ce sam ba za a bar Iran ko bai dace Iran da kungiyoyin ta su mallaki makaman ƙare dangi ba.

Abun dubawa shi ne yayin da Amurka da kasashen yamma ke takura Iran cewa lallai ta kunce ɗamarar ƙera makaman nukiliya, ga shi abokiyar hamaiyar ta a siyasance wato Isra’ila na mallakar makaman nukiliya da kai hare-hare duk inda ta ga dama da sunan yaƙi da maƙiyan ta.

Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da shugaban Sham Ahmad Al-Sharaa a birnin Riyadh.

An ga Trump na fuskantar Al-Sharaa da su ke musabaha cikin tamkar auna cewa wannan shi ya zama shugaban Sham.

Wannan dai takaitacciyyar ganawa su ka yi gabanin babban taron da zai haɗa dukkan shugabannin haɗin kan gabar ta tsakiya don tattaunawa kan ƙalubalen yankin.

Trump ya nuna Yarima Muhammad bin Salman ne ya ba shi kwarin gwiwar ya gana da Al-Sharaa don bude sabon babi ga Sham ɗin ta diflomasiyya da ƙasashen da ba sa ga maciji da juna da ita.

Donald Trump shi ne shugaban Amurka na farko a shekaru 25 da su ka wuce da ya gana da shugaban Sham.

Shugaban Amurka na ƙarshe gabanin wannan lokaci da ya gana da shugaban Sham shi ne Bill Clinton wanda ya gana da mahaifin hamɓarerren shugaban Sham Bashar wato Hafez Al’Asad a Geneɓa a shekara ta 2000 ya na mai fatar samar da sulhu tsakanin Sham da Isra’ila amma ganawar ba ta yi nasara ba.

Al’ummar Sham sun yi farin ciki da zummar dagewa ƙasar takunkumi da Trump ya yi inda su ka fito maza da mata dandalin Umayya a Damaskas su na farin ciki.

Al’Sharaa wanda ke da jini a jika ya zama shugaban Sham a watan Janairu bayan gwagwarmayar sa ta yaƙin sari ka noke ko sunkuru ya kawar da gwamnatin Asad da a ke dɗauka mai kama karya ga waɗanda ba sa bin muradun sa waɗanda mahaifin sa Hafez ya assasa a kasar.

Babban fata a nan Isra’ila ta dakatar da hare-hare cikin Sham don ba hannun Iran a yanzu kai tsaye a lamuran ƙasar sai dai akwai na Turkiyya.

Amurka da Katar sun rantaba hannu kan yarjeniyoyin harkokin hulɗar tattalin arziki da ta kai dala tiriliyan 1.2

Wato dai ƙasar Katar ta amince za ta zuba zunzurutun kuɗin nan don huldra cinikaiya da Amurka da hakan ya haɗa da sayo jirgen Boing sama da 200.

Wannan dai ya gudana ne a birnin Doha yayin da Trump ya ziyarci Katar daga Saudiyya inda akwai shiga Daular Larabawa ma.

Sarkin ƙatar Sheikh Tamim bin Hammad Al-Thani ne ya rantaba hannu a madadin kasar sa don ƙara inganta dangantaka da Amurka.

Sauran abubuwan da su ka tattauna sun hada da batun makaman kare dangin Iran, fitinar Yukrain da Rasha sai kuma shirin gasar Olympic da ƙwallon kofin duniya a Amurka a 2027.

A lokacin da Trump ke mulki wa’adi na farko yayin da Yarima Muhammad na Saudiyya ya rantaba hannu kan yarjeniyoyin sama da dala biliyan 300 a fadar White House, Katar ta caccaki Saudiyya da nuna tamkar ta na da ƙauyanci inda ta kan zuba kuɗi kan lamura marar sa riba.

ƙatar da Saudiyya sun yi tsama musamman daga 2017 na samun fifiko a yankin gabar ta tsakiya inda Katar ke amfani da kafar talabijin ɗin ta Aljazeera wajen cimma muradun ta. Aljazeera ta yayata dalilan da su ka jawo juyin juya hali a ƙasashen Larabawa.

Kammalawa;

Saudiyya a rigimar baya da a ka sulhunta ta zargi ƙatar da marawa Iran baya a lokacin wacce ba sa danyen ganye sai kuma ƙungiyar ‘yan Ikwan ta Hasanul Banna da ta taba samun nasarar kafa gwamnati a Masar da samun shugaba marigayi Muhammad Morsi.

Wannan ɗabi’a ta ƙatar ta sa Saudiyya ta kafa ma ta takunkumi mai tsauri da ma barazanar rufe tattalin arzikin ƙatar ɗin kirib sai da kyar a ka sulhunta don har ya shafi hana al’ummar ƙatar samun ɓISA ta hajji kai tsaye.

Bahrain, Daular Larabawa da ma Masar duk sun marawa Saudiyya baya wajen garkamawa ƙatar takunkumi.

Shin yanzu waɗannan manyan ƙasashen na Larabawa za su matsawa Trump lamba ya tilastawa Isra’ila ta daina kisan gilla a Gaza ba barin Gazawa su zauna lafiya a ƙasar su ta gado?

By ukarofi