Daga AISHA ASAS
Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ta bayyana damuwa kan matakin Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano na dakatar da finafinan Kannywood guda 22 da ba da shawara ga gwamnati da ta bi matakin hankali wajen irin waɗannan matakai.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na CITAD, YZ Ya’u ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa: “Ko da yake mun gane buƙatar kare tarbiyya da al’adunmu a ɗikin finafinan, dole ne a tabbatar cewa irin wannan mataki ba ya tauye ’yancin sadarwa na ’yan ƙasa ko kuma murkushe ’yancin ƙirƙira da fasaha.”
Ya ƙara da cewa: “A wannan zamani da intanet ke da matuƙar tasiri wajen ilimi, nishaɗi, da tattalin arziki, matasa da dama na amfani da kafafen sadarwa domin samun abubuwan nishaɗi daban-daban. Idan aka yi ƙoƙarin daidaita abubuwan sadarwa ba tare da la’akari da cikakken tasirinsu ba, hakan na iya mayar da masu ƙirƙira zuwa wasu hanyoyi ko masana’antun fim da ba su da irin shingayen tarbiyyar da ake ƙoƙarin karewa. A sakamakon haka, za a iya jefa matasa cikin kallon abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.”
CITAD ta kuma nuna damuwa da yadda take ganin ’yancin amfani da kafafen sadarwa ke kara yin ƙaranci a Jihar Kano. Ta kawo misalin kama Buhari Abba na Kano Times sakamakon wallafa bayanai a kafafen sadarwa, wanda a cewar cibiyar, ya kasance barazana ga ’yancin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Intanet fili ne mara iyaka, duniyar da ta hade mutane daga ko’ina cikin duniya. Babu wata jiha da za ta iya ware kanta daga wannan haɗin kai. Idan aka yi ƙoƙarin ware kai, hakan na iya sa ’yan fim ɗaukar finafinan su zuwa wasu kafafe da ke waje da ba ikon jihar ba.”
Daga ƙarshe, CITAD ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta yi la’akari da waɗannan abubuwa:
1. A tabbatar da ’yancin fadar albarkacin baki da samun bayanai kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
2. A guji matakai da ke tauye ’yancin amfani da fasahar sadarwa, domin hakan na iya hana ci gaban masana’antar ƙirƙira tare da ɓata sunan jihar.
3. Hukumar Tace FinaFinai ta Jihar Kano ta rungumi tsarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, irinsu masu shirya finafinai, ƙungiyoyin kare hakkin sadarwa da sauransu domin fitar da tsari mai adalci wanda zai kare al’adu da mutunta ’yancin jama’a a lokaci guda.
Wannan gargaɗi daga CITAD na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a faɗin Arewacin Najeriya dangane da yadda ake tafiyar da harkar finafinai da amfani da fasahar sadarwa.
