Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) reshen Jihar Gombe ta fito fili ta karyata ikirarin wani naɗin shugabanci bogi da ake dangantawa da ita, tare da gargadi kan wani taron sirri da ake zargin an shirya domin kawo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar.
A wata sanarwa da Ambasada Injiniya M. Abdulkadir Kumo, mai ba da shawara na musamman kan harkokin watsa labarai ga shugaban jam’iyyar na jiha ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa ba ta taba amincewa da naɗin Dokta Sadiƙ Abubakar Gombe a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa (Arewa) ba, tana kira ga jama’a su yi watsi da wannan ikirari da ta kira na bogi.
Sanarwar ta bayyana cewa Dokta Gombe ba mamba bane a jam’iyyar SDP bisa bayanan da ke hannunta, tare da tunatar da cewa a lokacin zabukan baya, yana tare da jam’iyyar PDP, ba tare da wata alamar ya dawo SDP ba.
Bugu da ƙari, jam’iyyar ta ambaci tsoffin ‘ya’yanta Musa Maccido da Reɓerend John Nwarke a matsayin waɗanda ke cikin shirya wannan taron da ba ta amince da shi ba, tana bayyana wannan matakin a matsayin rashin gaskiya da nufin kawo ruɗani.
SDP ta yi kira ga al’ummar gari da su yi fatali da duk wata sanarwa ko taro da ke alaƙa da wannan naɗin bogi, tare da sake jaddada cewa tana nan daram kan ƙudurinta na samar da jagoranci na gari ga ‘yan Nijeriya.
“Jam’iyyar SDP za ta ci gaba da kasancewa tsayayyiya, mai cike da nasara, tare da shirye-shiryen tsaf don zaɓen 2027, duk da irin waɗannan ƙoƙarin na kawo cikas,” sanarwar ta ƙarƙare.
