
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Furodusoshin Nijeriya (AMP) ta yi jimamin rasuwar Umar Maikuďi, Shugaban Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN).
AMP ta ce, rashin jagoran ƙungiyar babban giɓi ne ga ci-gaban harkar fina-finai a Nijeriya duba da irirn gudumawar da ya bayar a lokacin da ya ke raye.
A sanarwar da Shugabar ƙungiyar, Dakta Queen Blessing Ebigieson ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalai da ƴan uwa da abokan arziƙi gami da mambobin MOPPAN bisa babban rashin.
Ta kuma yi addu’ar Allah Ya yafe masa kurakuransa gami da sanya shi a Aljannar Firdausi.
AMP ta ƙara da cewa, irin gudumawar da ya bai wa masana’antar fina-finai, ba za a taɓa mantawa da ita ba, tana mai fatan Allah ya jiƙan sa da rahama.
