Najeriya ta casa Ghana a wasan kofin Unity

Spread the love

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta doke Ghana da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe na Unity Cup da aka buga a Gtech Community Stadium, London. Cyriel Dessers ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 14 da taimakon S. Ismail. Bayan mintuna biyar, ɗan wasan Ghana Razak Simpson ya ci ƙwallon kansa wanda ya ƙara wa Najeriya gagarumin rinjaye.

Ghana ta samu nasarar jefa ƙwallo guda a minti na 70 ta hannun ɗan wasanta Thomas-Asante, wanda hakan ya sa wasan ya ƙare da ci 2-1. Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar samun gurbi a wasan ƙarshe na Unity Cup inda za su kece raini da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamaica.

Unity Cup wani gasa ne da ke haɗa ƙasashen duniya don ƙarfafa zumunta ta hanyar ƙwallon ƙafa. Wannan nasara na Najeriya ya nuna yadda tawagar Super Eagles ke ci gaba da ƙoƙari wajen dawo da martabarta a ƙasashen duniya, musamman ma bayan canjin dabarun wasa da ƙungiyar ta yi.

By ukarofi