Shugaban majalisar wakilai ya janye ƙudurin yin dokar tilasta wa ‘yan Nijeriya yin zaɓe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya sanar da janye ƙudurin dokar tilasta yin zaɓe ga waɗanda shekarunsu ya kai su yi zaɓe a Nijeriya.

Musa Krishi, mataimaki na musamman ga shugaban majalisar, ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

An fara gabatar da ƙudurin gyaran dokar zaɓen 2022 domin tilasta wa ‘yan ƙasa zaɓe a watan Fabrairu ta hannun shugaban majalisar tare da Daniel Ago, wanda ke wakiltar mazaɓar Bassa/Jos ta Arewa.

Dalilin janye ƙudurin:

Tajudeen ya ce an ɗauki matakin janye ƙudurin dokar ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ɓangarori daban-daban.

“Ya yanke shawarar janye ƙudurin dokar gyaran dokar zaɓe wacce zai tilasta wa ‘yan Nijeriya da suka kai munzalin yin zaɓe da suka gabatar shi da Ago.”

“Tun da fari, an gabatar da ƙudurin ne da kyakkyawar niyya domin ƙarfafa wa al’umma da dimokuraɗiyya wajen samun yawan masu kaɗa ƙuri’a,” ya faɗa.

Ya ce, dokar tilasta yin zaɓe ana yin ta a ƙasashe kamar Australia, Belgium da Brazil kuma an ga fa’idarta.

A cewarsa dokar yin zaɓe dole ta taimaka wajen samun sama da kaso 90 da kan fito su kaɗa ƙuro’unsu a ƙasashe kamar Argentina da Singapore kuma shi ma shugaban majalisar ya kawo ƙudurin ne saboda cimma irin waccen nasara.

Sai dai Tajudeen ya ce kowacce doka da za a yi ta ta’allaka ke da mutanen da za a yi wa ita, kuma yana da kyau a mutunta ‘yancin kowanne mutum da ra’ayin al’umma.

“A maimakon tilasta wa al’umma fitowa zaɓe, yana tunanin lalubo wata hanya ta jan hankalin al’umma da zai sa su yin dafifi wajen fitowa zaɓe a Nijeriya.”

“Wannan janyewa za ta ba da dama domin a samu tattaunawa ta samar da tsarin fita yin zaɓen domin raɗin kai ta hanyar dimokuraɗiyyar da ‘yancin ɗan ƙasa.”

Game da ƙudurin gyaran dokar zaɓe:

‘Yan majalisa Tajudeen da Ago ne suka gabatar da ƙudurin dokar a majalisar a watan Fabarairu.

Bayan tattaunawa, ƙudurin dokar ya tsallake karatu na biyu a wannan wata kuma har an miƙa shi ƙudurin ga kwamitin kula da harkokin zaɓe a majalisar.

ƙudurin ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya da suka ƙi kaɗa ƙuri’a za su fuskanci hukunci na zaman kaso na watannu 6 ko biyan tara na Naira 100,000.

A yayin muhawarar, Ago ya ce, tilasta yin zaɓe zai ƙarfafa dimokraɗiyyar a Nijeriya ta hanyar ƙarfafa wa al’umma guiwar gudanar da zaɓe da magance matsalar rashin nuna sha’awa da inganta sahihancin zaɓe.

Game da nuna ƙin amincewa da ƙudurin:

Sai dai ƙudurin ya jawo ka-ce-na-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya kan irin tasirin da hakan ke da shi ga ‘yancin gundanar da dimokraɗiyya da kare ‘yancin ɗan’Adam.

ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta bayyana wannan doka da wadda ta saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma tauye ‘yancin ‘yan ƙasa.

A cikin wani jawabi da shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe, ta sanya wa hannu, ya ce, ƙudurin dokar ya saɓa wa ‘yancin ɗan’adam wanda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 wanda zai tauye tsarin dimokraɗiyya.

Ita ma ƙungiyar da ke sa idao da wayar da kan jama’a Yiaga Africa, ta ce wannan ƙuduri zai saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Babban daraktan Yiaga, Sam Itodo, ya ce duk da wannan ƙuduri na ƙoƙarin magance ƙarancin masu kaɗa ƙuri’u, sai dai wannan ƙuduri ya saɓa da ‘yancin ɗan’Adam.

“ƙudurin ya ƙunshi ƙoƙari na magance matsalar rashin fitowa zaɓe. A yayin da manufar wannan ƙuduri shi ne magance babbar matsalar da ke damun tsarin zaɓe na Nijeriya. Sai dai babban matakin da ƙudurin ya tanada ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da ‘yancin ɗan’Adam,” inji Itodo.

Game da janye ƙudurin:

Wannan ne karo na biyu da Tajudeen yake janye ƙurin doka da yake gabatarwa a majalisa.

A watan Agustan 2024, ya janye ƙudurin da zai sa a riƙa ɗaure mutane da suka ci mutucin jami’an gwamnati.

“Sakamakon irin yadda al’umma suka bayyana ra’ayoyinsu kan ƙudurin, shugaban majalisar wakilan, Abbas Tajudeen, PhD, ya yanke shawarar janye ƙudurin da duk wata doka da ta danganci hakan.”

“Wannan mataki ya biyo bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da duba na tsanaki da muka yi kan yanayin al’amura na ƙasa,” a cewar majalisar a shafinta na X.

By ukarofi