Tinubu na shirin raba mitocin lantarki miliyan bakwai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin raba mitoci miliyan bakwai ta hanyar shirin ta na Shugaban ƙasa, da nufin kawar da matsalar cajin kwastamomi na wuce kima da kuma rage samun giɓi a kuɗaɗen shiga.

Mataimakiya ta musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin lantarki, Olu Verheijen, ta bayyana hakan a wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Abuja ranar Lahadi.

Da take magana kan bikin cika shekaru biyu na gwamnatin Tinubu, Verheijen ta bayyana cewa, mitoci na zamani za su kawo ƙarshen asarar da yawancin abokan cinikin su ke yi.

Ta bayyana cewa tura mitoci wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnati ke yi na inganta sarkar kimar kasuwancin iskar gas zuwa lantarki.

“Akwai wasu matakai da yawa da ake gudanarwa don haɓaka kasuwancin iskar gas zuwa wutar lantarki.”

Mashawarciyar na musamman ta kuma bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin ta biya basussukan da ake bin ta, wanda ya taru sakamakon rashin samun tallafin wutar lantarki da kuma yadda kamfanonin rarraba (Discos) suka gaza wajen tara kuɗaɗen shiga.

By ukarofi