
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin ƴan Nijeriya guda 35 har da yara ƙanana ne ƙasar Jamhuriyar Ireland ta koro su dawo wa Nijeriya daga filin jiragen sama na Dublin a ranar Laraba.
Irish Mirror ta ruwaito cewa, mutanen sun haɗa da maza guda 21 da mata tara da yara ƙanana biyar, waɗanda suka iso Nijeriya a ranar Alhamis.
Ministan Shari’a na ƙasar, Jim O’Callaghan ya ce ya yi farin ciki da yadda dukkan su suka koma Nijeriya duk da cewa an samu tsaiko a hanya a sakamakon al’amarin lafiya da ya bijiro.
Gwamnatin ƙasar ba ta bayyana haƙiƙanin dalilin koro ƴan Nijeriyar ba, saidai ministan shari’ar ya ce ƙasar tana da dokoki da tsare-tsare na shige da fice don haka yana da muhimmanci a kiyaye su.
Akan haka ne Hukumar Kula da Lamuran ƴan Nijeriya dake Waje (NiDCOM) ta ce ba ta san da batun maido da mutanen ba daga Ireland.
Kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya bayyana wa Punch Diaspora Tales hakan a ranar Alhamis.
