Mece ce cutar sanyin mara?

Spread the love

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Cutar sanyin mara (a Turance: Pelvic Inflammatory Disease – PID) wata cuta ce da ke kama sassan haihuwa na ciki a jikin mace, inda yana faruwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta daga farji ko mahaifa suka hau sama zuwa cikin mahaifa da sauran sassan ciki.

Abubuwan da ke jawo cutar sanyin mara, watau ‘infection’:

1. Cutar kan yaɗu ta hanyar saduwa da mace ko namiji mai ɗauke da cututtukan saduwa, kamar su ‘chlamydia’ da ‘gonorrhea’.

2. Rashin tsafta yayin amfani da abubuwan tsaftace al’aura.

3. Yawan saduwa da mutane barkatai.

4. Amfani da kayan hana ɗaukar ciki irin su ‘IUD’ ba tare da kulawa daga likita ba.

5. Zubar da ciki ko haihuwa ba tare da tsafta da kula ba.

Alamomin cutar sanyin mara:

1. Yawan ciwon mara

2. Yawan zubar ruwa mai wari daga al’aura

3. Jin zafi yayin yin jima’i.

4. Jin ɗafi yayin yin fitsari.

5. Zubar jinin al’ada mai yawa ko da ba lokacin al’ada ba.

6. Zazzabi da jin kasala.

Illolin cutar idan ba a magance ba:

1. Rashin haihuwa (infertility).

2. Ciwo kullum a ƙasan ciki, wato ciwon mara.

3. Samun ciki a wajen mahaifa (watau ‘ectopic pregnancy’)

4. Shigar ƙwayar cuta cikin jini, wanda ke da matuƙar haɗari ga lafiyar mace.

Hanyoyin kariya daga wannan cuta ta ‘infection’ ko sanyin mara ta mata:

1. Guje wa saduwa da mutum da ke da ƙwayoyin cutar saduwa da ake iya ɗauka, watau ‘seɗual transmissted diseases’.

2. Yin amfani da kwaroron roba (condom) yayin saduwa da mutane barkatai.

3. Zama da abokin saduwa guda ɗaya.

4. Kula da tsafta yayin jima’i da bayan al’ada.

5. Kulawa da al’ada ta hanyar ganin likita idan ki na fuskantar alamomin cutar.

By ukarofi