Matashi ya bi matar aure har gidanta ya yanka ta da wuƙa

Spread the love

Matashi ya bi matar aure har gidanta ya yanka ta da wuƙa’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano.

A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar kama wanda ake zargin mai shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai ne a ranar 23 ga watan Mayu ta hanyar binciken sirri.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a hannun ’yan sanda, inda ya bayyana cewa ya shiga gidan wadda aka kashe ne ya shake ta, sannan ya soka mata wuƙa a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Sanarwar ’yan sandan ta ce, “za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.”

Lamarin mai ban tausayi ya bayyana ne lokacin da mijin matar mai suna Ibrahim Mohammed, ya tsinci gawarta da mummunan rauni a wuyanta.

An garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Rundunar ’yan sandan ta yaba wa jami’anta masu bincike saboda ƙwarewarsu da kuma jajircewarsu wajen cafke wanda ake zargi, inda ta ƙara da cewa ana ci gaba da bincike don tabbatar da an yi cikakken adalci.

By ukarofi