Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta koka kan lalacewar hanyar Funtua zuwa Ɗandume

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hanyar mai tsawon kilomita 45 ta wuce zuwa Birnin Gwari ta miƙa har zuwa Legas.

Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman yayi wannan koken ne a saƙon sa na barka da sallah ga al’ummar Jihar Katsina.

Ya bayyana cewa al’ummar yankin Ɗandume manoma ne kuma sun dogara da wannan hanya wajen fitar da amfani gonar su zuwa wasu jihohin ƙasan har da Jihar Legas.

“Amma saboda rashin kyawun hanyar manyan motocin da ke ɗaukan amfanin gonan zuwa waje sun bar zuwa saboda rashin kyawun hanyar wanda hakan ya jawo wa manoman mummunan asara”, inji kwamred Suleiman.

Sai yayi kira ga gwamnatin jihar,Sanata Ɗandutse da ‘yan majalisar yankin da su haɗa karfi da ƙarfe wajen tunkarar gwamnatin tarayya da ta zo ta gyara ko gina sabon hanyar domin dawo da harkokin noma da kasuwanci a yankin.

Kwamred Suleiman ya yabawa wa gwamna Dikko Raɗɗa kan ƙoƙarin da yake wajen magance ta’addancin da sanya matasa a harkokin tafiyar da gwamnatin sa.

Ya ce ƙungiyar su a shirye take ta haɗa kai da gwamnatin Dikko Raɗɗa wajen bada gudunmawar shawarwari na cigaban jihar musamman yankin Funtua.

Wannan hanya da ake kira ‘mutuwa kusa’ ta janyo mutuwar mutane da dama da salwantar ɗinbin dukiya da ƙaruwar ta’addanci bama a Ɗandume ba har yankin Funtua baki ɗaya.

By ukarofi