
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da bincike akan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, wanda ke nuna yadda aka yi sakaci da al’amarin wasu marasa lafiya da suka yi hatsari a ɗakin agajin gaggawa na Babban Asibitin Tarayya (FMC) dake Jabi a Abuja.
Bidiyon ya bayyana yadda aka bar marasa lafiyar kara zube ba tare da kula su ba duk da cewa an kai su ne a mawuyacin hali daga aukuwar hatsarin.
Wanda ya ɗauki bidiyon ya ce, an samu mutanen ne a hali na jikkata, inda ya ɗauke su zuwa asibitin domin ba su kulawa ta gaggawa.
Ya yi zargin cewa, jami’an asibitin sun ƙi sauraron su, inda ɗaya daga cikinsu ya ce sun yi haka ne saboda babu safar hannu da za su fara aiki da shi.
Hallau, a bidiyon ne aka ga yadda wasu ma’aikatan asibitin suke ƙoƙarin ɗaga wani da ya samu munanan raunuka da nufin kai shi ɗakin kulawar gaggawar.
Wasu kuwa da kansu suke daddafawa suna zuwa ɗakin duk da raunukan da suka samu.
A yayin bada amsa game da lamarin, jami’in hulďa da jama’a na asibitin, Obadiah Gana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce hukumar gudanarwar asibitin ta fara bincike akan al’amarin.
Sakamakon da aka gabatar a karon fari ya bayyana cewa, asibitin yana da isassun kayan aiki da ma’aikatan da za su kula da ɓangarenba tare da sum tsaiko ba.
